MANUFOFIN YIN KWANAKI BAKWAI A ƊAKIN BUDURWA, KWANA UKU A ƊAKIN BAZAWARA IDAN AN YI SABON AURE

▪️📚 MANUFOFIN SHARI'AR MUSULUNCI 12 📚▪️

✍️ Yusuf Lawal Yusuf

MANUFOFIN YIN KWANAKI BAKWAI A ƊAKIN BUDURWA, KWANA UKU A ƊAKIN BAZAWARA IDAN AN YI SABON AURE



Ya zo a cikin hadisin da Tirmidhi ya rawaito daga Anas: "Yana daga cikin Sunna, in mutum ya auri budurwa kuma yana da wata matar, ya zauna a ɗakinta tsawon kwana bakwai; idan kuma ya auri bazawara ya zauna tsawon kwanaki uku tare da ita." Abin tambaya anan shi ne: me yasa aka bambanta tsakanin budurwa da bazawara? 

1. Kwantarwa da budurwa hankali. 

2. Ɗebe mata kewa. 

3. Gusar mata da jin kunya, saɓanin bazawara wacce dama ta saba da maza, don haka kwanaki uku sun ishe ta. 

Tsakure daga cikin littafin Manufofin Shari'ar Musulunci, wallafar Sheikh Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

*18th Rajab, 1442A.H (02/03/2021).*
Post a Comment (0)