KADA KA DAMU



KADA KA DAMU.
-
"A lokacin da ka shiga cikin wani halin razani da rashin aminci, to kada ka kuskura kace wani ne zai iya amintar dakai ya kuma warware maka damuwar ka in ba Allah ba"
-
"Allah maɗaukakin sarki shine wanda yake koda yaushe yana tareda bayinsa, da jinsa, da ganinsa, da kuma taimakonsa, idan ka yarda dashi, kabi matakan haƙuri da yarda da ƙaddara, sai ya taimaka maka ya kuma baka aminci"
-
"Ka kawar da dukkanin damuwar da take damunka, ka mayar da dukkanin ilahirin lamuranka zuwa ga Allah, lallai ne Allah yana tareda bayinsa a duk inda suka tsinci kansu, tarayya irin wacce ta dace dashi, haƙiƙa shine wanda zai yi maka maganin dukkanin damuwar ka, ƙunci, baƙin ciki, damuwa, firgici, tsoro, razani, talauci, dukkanin su Allah ne wanda yake riƙe da iko akansu, to ka yarda shine zai iya baka aminci daga garesu, haƙiƙa shine mafi alkhairin masu warware damuwar bayinsa"
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
Post a Comment (0)