ƊAN ADAM KENAN!



ƊAN ADAM KENAN!
-
"Ɗan adam mutum ne mai taurin kai da gardama da kuma nuna taƙama, an samar dashi daga wani ƙazamtaccen ruwa (maniyyi) sai daga baya Allah maɗaukakin sarki ya kyautata halittarsa, ya kuma karrama shi, amma kuma ƙarshe duk ya manta da asalinsa"
-
"Kullum yakan zaƙewa saɓon mahaliccinsa Allah, yakan raina bayinsa ya ƙasƙanta su, gani yake tamkar shine wanda yafi kowa acikin halittun Allah buwayi, ya manta da cewa babu wani ɗaya da yafi wani a gurin Allah face sai wanda yafi kowa tsoron Allah, kuma kullum shi saɓo yake aikatawa tamkar baya tunanin mutuwa"
-
"Dukkanin wanda aka halitta, to haƙiƙa shi matacce ne, dukkanin mu daga Allah muke kuma gareshi muke komawa, dukkanin mu da ƙasa aka halicce mu, kuma cikinta ake mayar damu, haƙiƙa babu taƙama da jiji dakai ga wanda yasan makomarsa cikin ƙasa ne"
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6osqg5
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
Post a Comment (0)