LAGAAN YA CIKA SHEKARU 20 DAIDAI DA FITA



LAGAAN YA CIKA SHEKARU 20 DAIDAI DA FITA:

Hakan Ya Zama Kamfanin Jarumi AAMIR KHAN Watau Aamir Khan production ya cika Shekaru 20 Kasanwar Lagaan da ya Fita 2001 Shine Na Farko..

Jarumi Aamir Khan Yace Lokacin da Yake Shirin Yin Wannan Film Abokanansa da Suka Kasance Manya-Manya Wajen Shirya Films Watau Karan Johar da Aditya Chopra Sunce Zaiyi Babban Kuskure Matuqar Yayi Wannan Film Domin Ba Karamin Film bane ba Amma duk da Haka Sun Bashi Shawarwari Wanda Yake Alfahari Dasu..

Jarumi Aamir Khan Yace Akwai Abubuwan da Yake Matuqar So Ya Aiwatar Acikin Films Amma Kasanwar ba Yanda Zaiyi Hake Yake Haqura Har Lokacin da Ya Samu Damar Yin Wannan Film Ya Aiwatar Dasu.

Wannan Film Ya Samu Duk Wata Nasara da Ake Bukata Acikin Finan-finai Kamar Samu Yabo Daga Masana Films da Yan Kallo da Samun Gagarumar Nasara a Kasuwanci Sannan.

LAGAAN ya Fito da Kimar Bollywood a 2002 Bayan Ya Shiga Jerin Masu Takarar Karbar Oscar Award Watau Gasar Finan-finan Duniya Sannan Ya Zama Film Daga Cikin Jerin Wasu Finan-finai da Akace Dole Ka Kalla Tun Kafin Ka Mutu.

Duk da Aamir Khan Yace Yana Tsoron Shirya Films Tun Asali Saboda Mahaifinsa Tahir Husain da Kawunsa Nasir Husain Suma Suna Shiryawa Yasan Yanda Suke Shan Fama Musamman Wajen Kudi Inda Yace da An Kuskure Akwai Lokacin da Suka Kusa Komawa Rayuwar Kan Titi Domin Daman Ga Duk Masu Bibiyar Finan-finan India Sun San Cewa Mahaifinsa Tahir Hussain Bashi da Nasara Wajen Shirya Films.

Aamir Khan dai Bayan Ya Shirya Lagaan Kuma Daga Bisani Duk a Karkashin Kamfanin sa Yayi Finan-fina da Kowane Idan Yayi Ya Samu Nasara Domin Taare Zameen Par Shine Na Biyu Wanda Kuma Suka Fita Kwanan Nan Sune Dangal da Secret Superstar Yanda Kowa Yasan Irin Nasarar Da Suka Samu.

Kamfanin Suna Shirya Film Yanzu Haka Me Taken LAL SINGH CHADDHA Wanda a Yau Sun Dora Wani video Da AAMIR KHAN ya Bayyana da Kayan Manyan Sojoji Inda Yake Magana Akan Nasarar Shi Lagaan Sannan Yace Yanzu Haka Daga Aikin Wannan Film ya Gama na Wannan Rana Yake Wannan Bayanin.

By #AbbaIndiaDala


Post a Comment (0)