MACE ZA TA IYA YIN I'ITIKAFI ?
Tambaya:
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh malam menene hukuncin ittikafin mata a musulunchi?
Amsa:
Wa alaikum asssalam, ya halatta mace ta yi i'itikafi, saboda matayan Annabi s.a.w sun yi I'itikafi kamar yadda ya zo a sahihil Bukhari.
Yana daga cikin ka'idoji a usulul fiqhi duk hukuncin da ya zo a sharia yana hade mata da maza, sai idan an samu dalilin da ya kebance maza kawai.
I'itikafi ibada ce tabbatacciya a musulunci wacce Annabi s.a.w. ya aikata ta saboda neman kusanci da Allah a watan Ramdhana, babu banbanci tsakanin mace da namiji wajan koyi da Annabi s.a.w a wannan ibadar, saidai kar matar aure ta fita sai ta nemi iznin mijinta.
Allah ne mafi sani.
28/6/2016
Dr Jamilu Zarewa.
Zaku iya bibiyar mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248