Muji tsoron Allah yan uwa Musulmai



Muji tsoron Allah yan uwa Musulmai

Yara su girmama manya
Manya su tausayawa Yara

Daliba ayi karatu a daina satar amsa

Malamai su daina zalunci

Yan gwamnati a guji girman kai

Yan kasuwa a ci halali a jikan al'ummah

Jami'an tsaro a daina rashawa da cin hanci

Kamfanoni da masana'antu a daina algussu

Iyaye a kula da ya'ya da Yan uwan su

Ma'aurata a dinga hakuri da juna

Samari a daina shaho in kayi za'a yi ma

Yan mata a daina yaudara in kin yi kan ki

Yan jarida a fadi gaskiya a guji toge

Yan shari'ah a guji rashawa da cin hanci

Ma'akatan lafiya a ji tsoron Allah, a raba maganin gwamnati kyauta, a daina zubar da ciki babu dalili, a daina kara ma marasa lafiya ciwo don samun kuddi, a daina yawan basge mutane saboda kuddi.

Yan siyasa a daina walakantar da al'ummah, a guji handama da baba kere, a kula da al'ummah, a ingantar da jin dadin al'ummah.

Dukkanin mu za'a tambaye mu, abinda muka aikata shi zamu gani, in kharan in sharran.

Allah yasa mu gama da duniya lafiya

*JUMU'AT KAREEM YAN UWA MUSULMAI*
_Zayyanu haruna #
Post a Comment (0)