ADDU'A DON SAMUN MIJIN AURE
*TAMBAYA*❓
Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu mallam inasan asani acikin addu'a bani da miji ina cikin damuwa sosai akan wnnan matsala kuma ina iya bakin kokari na akan addu'a amma abu yaci tura malam sai naji amsarka.
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Da farko dai ina tayaki alhini bisa wannan matsanancin halin da kike ciki. Kuma ina mai yin nasiha agareki cewa ki sani kowanne abu yana da lokacinsa wanda Ubangijiya riga ya Qaddara agareshi.
Kuma abubuwa suna gudana ne bisa gwargwadon yadda Ubangiji Allah Ya Qaddara kuma yaso su faru.
Bai kamata ki rika tunanin cewa wai kin roki Allah, Kin roki Allah, amma abu yaci tura ba.. Allah ba ya son bawansa ya rika furta wadannan kalmomin.
Annabi (saww) yace : "ZA'A AMSA MA 'DAYANKU (ADDU'ARSA) MUTUKAR BAI YI GAGGAWA BA, SHINE IDAN YACE "HAKIKA NAYI ADDU'A AMMA BA'A AMSA MIN BA".
Ki dogara ga Allah ki sani cewa baki da wani Ubangijin sai SHI. Kuma idan bai yi miki ba, babu wanda ya isa yayi miki.
Ki kyautata zatonki ga Allah. Domin hakika shi Allah masoyin bayinsa ne, Mai karamci ne, Kuma shi mai kyauta da baiwa ne.
Manzon Allah (saww) yace : "HAKIKA UBANGIJINKU MAI KUNYA NE, MAI KARAMCI NE. YANA JIN KUNYAR BAWANSA YAYIN DA YA CIRA HANNAYENSA YA ROKESHI, ACHE YA MAYAR DASU BA TARE DA KOMAI BA".
Don haka ki kyautata tunaninki. Hakika Allah ya riga ya amsa miki. Kawai lokacin ganin abun ne bai Qaraso ba. Ki Qara hakuri kuma kiji tsoron Allah ki kiyaye dokokinsa.
Ki yawaita salati da tasleemi bisa Annabinsa (saww) domin salati agareshi babbar hanyar samun yayewar damuwa ce.
Ki rika yin wannan addu'ar :
" ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺍﻟﻬﺪﻯ ﻭﺍﻟﺘﻘﻰ ﻭﺍﻟﻌﻔﺎﻑ ﻭﺍﻟﻐﻨﻰ .".
"ALLAHUMMA INNEE AS'ALUKAL HUDA WAT-TUQA WAL 'AFAF WAL GHINA".
Ma'ana : "Ya Allah ina rokonka shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da kuma wadata".
Kuma ki yawaita Istighfari sosai domin shima babbar hanyar samun ijabah ne.
In sha Allahu Ubangiji zai azurtaki da samun Miji nagari, nan bada jimawa ba.
WALLAHU A'ALAM.
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248