BAMBANCI {11}



BAMBANCI {11}

Bayan iyaye sun kula wajan tarbiyyantar da yaransu karanta Addu'o'in neman tsari waɗanda Shari'a ta tabbatar da su, sai kuma su yunkura wajan nuna musu abubuwan da shari'a ba ta so kuma ba ta maraba da su hasali ma su ne ke jawo iskokai, makarai ko kuma Aljanu su aboci mutum ta ko wacce irin fuska kamar: Sanya tufafin da basu dace da Shari'a ba, kallace-kallacen abubuwan da Shari'a take kyama kuma ta haramta da dai sauransu.

A rubutu na 10 munji wasu daga cikin alamomin da ake gane karamar yarinya na tare da Jinnul Aashiq, shin ya za ayi kuma a gane alamar Jinnul Aashiq ga budurwa wacce batayi Aure ba kuma me ke kawo su?

Farko dai ya kamata mu san irin dokokin da Shari'a ta gindaya mana, musan abinda ALLAH yake so da wanda ba ya so, saboda babu abinda Shari'a ta bari batayi bayaninsa ba kuma Manzon Allah salllahu alaihi Wasallama bai bar duniya ba sai da ya nuna mana duk wani Alkhairi domin mu jibince shi kuma mu aikata shi, kuma ya nuna mana duk wani sharri domin mu guje shi kuma kar mu aikata shi.

Daga cikin abinda ke jawo Jinnul Aashiq ga budurwa wacce batayi aure ba, ga kadan daga cikinsu nan:

1- Fitar da tsiraici, ta rika shiga ta banza, ko kuma ta sanya tufafi amma kamar bata sanya ba, saboda surorin jikinta sun bayyana, ( domin su jinsin maza Aljanu sunfi sha'awar jinsin mata na mutane sama da yadda jinsin maza na mutane ke sha'awar jinsin mata na mutane yan uwansu,)

2- Barin kai abude indai ba da wata sananniyar lalura ba, sai kaga ko kanta ne abude ko wani bangare na gashin kanta ya fito waje sai kaga su Aljanun sun fitinu da ganin gashinta ya basu sha'awa, sabanin jinsin mutane maza ba kasafai ganin gashin mace ke sanya su fitinu da ita har suyi sha'awarta ba.

3- Rashin yin Addu'a idan za'a shiga Toilet (Ban daki).

4- Rashin yin Addu'ar tube tufafi ( Akalla kice *Bismillahi* idan za ki cire riga ko zabi ko wando ko makamantan su), domin ita "Bismillahi" ALLAH yana sanya katanga tsakanin idanuwan shedanu da kuma al'aurar mutum, ta yadda su Shedanun ba za su iya samun damar ganin al'aurar cutar da duk wanda ya furta ta kafin ya cire tufafin sa ba balle kuma su cutar da shi.

5- Yin istimna'i ( Mutum taruka biyawa kansa bukata da hannu ko da wani abu makamancin haka, har a gamsu ko akasin haka).

6- Zancen batsa ta ko wace irin sifa da kuma kallon batsa.

7- Kauracewa karatun Alqur'ani da Azkaar na safiyar da maraice da kuma wajan kwanciya bacci da kauracewa saurarar wa'azi da Kuma yawan sauraron kade-kade da wake-wake.

8- Bayyana kwalliya ga jama'ar a makaranta ko a waje ko kuma a kasuwa ko dora hoto a social media tare da bayyanar da wani bangare na kwalliyar ki a fuska ko a hannu ko makamantan haka, ( Kamar mace tayi lalle a hannunta ko kafarta har ta rika bayyanar da su ga jama'a ko a social media) , a Irin haka ba wai iya mutane ne kaɗai za su kalla ba har Aljanu ma suna kalla kuma idan kin ba su sha'awa sai su shafe ki su cutar da ke .

9- Rashin kamun kai ga mace yazamto kowa kulawa take, tayi ta cin chewing gum akan hanya ko tana tafiya tana ciye ciye ko tarika shekewa da dariya abinta, yin hakan yana iya sabbaba mata shafar shedanu.

10- Wata kuma za kaga tana kiyaye duk wannan abubuwan daidai gwargwado amma kuma sai ka same ta da Jinnul Aashiq, to ita wannan ana sa ran Sihiri ne aka yi mata. ALLAHu A'alam.

Wannan kadan kenan daga cikin abinda ke janyowa mace Jinnul Aashiq ko sihiri har suyi tasiri ajikinta, yanzu wace Alama ce mace za ta iya ganewa tana da shafar Jinnul Aashiq ajikinta?

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji bayanin nan.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
Post a Comment (0)