Ramadaniyyat 1442 [20]
Dr. Muhd Sani Umar (Hafizahullah)
Babbar Ni'imar Allah Ga Sahabbai (3)
______________________________
1. Allah (SWT) ya ce: (Ya ku wadanda suka yi imani, idan kuka bi wani bangare na wadanda aka ba wa Littafi, to za su mayar da ku kafirai bayan imaninku.) [Ali Imran: 100].
2. Wadanda suka yi imani a nan, ana nufin sahabbai 'yan kabilar Ausu da Khazraj. Alhil kitabi kuma ana nufin Yahudawa.
3. Allah ya nuna musu cewa idan suka yarda suka biye wa wadannan, to babu abin da za su saka su face su mayar da su irin rayuwarsu ta da, rayuwarsu ta fadace-fadace. Allah ya nuna musu suna da wata daraja wacce da can ba su same ta ba, ita ce darajar imani, yanzu sun yi imani da Allah ba su da abin bauta da gaskiya sai Allah shi kadai; sun yi imani da Manzon (SWT) a matsayin shi ne Annabin da Allah ya zaba ya aiko shi ya shiryar da shi. Sun yi imani da littafin da ya aiko muku shi ne Alkur’ani. Hakanan sun yi imani da ranar Lahira wanda a da can ba su yi imani da wadannan abubuwa ba.
4. Su kuma Yahudu sun kyale su, duk da su sun yi imani da samuwar Allah, sun yi imani da annabawan Allah, sun yi imani da ranar lahira, to amma sun ki yarda su saka wani a cikin addininsu, domin suna ganin su addininsu addini ne na zababbu. Sauran mutane kuwa kamar bayinsu suka dauke su. Kuma addininsu ya halatta masa su zalinci duk wani wanda ba bayahude ba. Kuma su kadai Allah yake so, kamar yadda Allah yake cewa game da su: (Kuma Yahudawa da Nasara suka ce: “Mu ‘ya’yan Allah ne, kuma masoyansa.) [Ma’ida: 18].
5. Saboda haka suna iya cin mutuncin mutum, ko su ci dukiyarsa, ko su jikkata shi, ba tare da suna tunanin akwai hisabi ba, saboda suna daukar kansu a matsayin zababbun Allah: (Kuma daga cikin Ma’abota Littafi akwai wanda in da za ka ba shi amana ta dukiya mai yawa, zai dawo maka da ita, daga cikinsu kuwa akwai wanda idan da za ka ba shi amana ta dinare daya, ba zai dawo maka da shi ba, sai fa idan ka tashi tsaye a kansa. Wannan kuwa saboda sun ce: “Babu wani laifi a kanmu (don mun ci dukiyar) bobayin mutane.” Kuma suna fadin karya su jingina wa Allah, alhalin su suna sane.) [Ali Imran: 75].
6. Hakan ya sa zamansu a Madina ba su mayar da hankali wajen su ga sun shigar da mutanen Madina cikin addininsu yahudanci ba, a’a sai dai su yi amfani da damar da suka samu su karawa kansu karfi da tattalin arziki a Madina.
7. Shi ne Allah yake fada wa kabilu biyun cewa ku kun yi imani. Shi yasa ya kira su da sunan imani ya ce: (Ya ku wadanda suka yi imani, idan kuka bi wani bangare na wadanda aka ba wa Littafi, to za su mayar da ku kafirai bayan imaninku.) [Ali Imran: 100]
8. Sai Allah (SWT) ya ba wa sahabbai wata daraja da kariya, kariyar da ba za ta bari su koma ga kafirci ba, ba za ta bari su koma ga jahilci ba. Za su ci gaba da tsayuwa a kan imaninsu da Musuluncinsu. Sai Allah ya ce: (Ta yaya kuma za ku kafirce, ga shi kuwa ana karanta muku ayoyin Allah, kuma Manzonsa yana tare da ku? Duk kuwa wanda ya riki Allah, to hakika an shiryar da shi tafarki madaidaici.) [Ali Imran: 101].
9. Wadannan darajoji guda biyu da Allah ya yi wa sahabbai su ne cewa, ba zai yi wu su koma ga kafirci ba bayan wadannan darajoji da ya yi musu, ko kuma su koma irin rayuwarsu ta baya ta jahilci ko ta munafurci da rashin gaskiya. Shi ya sa Allah ya bude ayar da sigar tambayar da ake cewa istifham lil istib’ad, ma’ana, ta ya ya ma za ku kafirta? Watau ba zai taba yiwuwa ba a ce kun kafirta ga shi ana karanta muku littafin Allah, su ne wa’azuzzuka da ku ke ji daga bakin Annabi (ï·º) da Alkur’anin da yake karanta muku da hadisansa da hudubobin da yake yi muku, kuke jin su duk sati daga bakin da yafi kowane baki gaskiya, kuka yarda cewa, Annabin Allah ne, to ta ya ya kuna jin wannan za ku yarda ku kafirta?! Ba zai yi wu ba.
10. Sannan abu na biyu shi ne: (kuma Manzonsa yana tare da ku) [Ali Imran: 101]
11. Watau a cikinku ga Manzon Allah yana tare da ku. Wannan ma matsayi ne wanda ba zai bari a ce kun koma ga kafirci ba.
12. Wannan yana nuna cewa, sahabban Annabi (ï·º) sun samu kariya daga komawa zuwa ga kafirci ko aikin kafirci ko aikin kafirai, sabod
https://t.me/miftahul_ilmi