NA HADU DA BUDURWA A FACEBOOK, TANA SO NA, INA SON TA, A BANI SHAWARA!!!



TAMBAYA TAMBAYA TAMBAYA

NA HADU DA BUDURWA A FACEBOOK, TANA SO NA, INA SON TA, A BANI SHAWARA!!!

Assalamu alaikum Warahmatullah wabarakatuhu. Dafatan malam da iyalan malam suna lpa, Allah yasa haka Amin summa Amin. Don Allah malam aeta haquri damu. Malam ga tambayata gareka:
Malam Allah yahadani dawata yarinya a Facebook, to malam tace tana sona kuma nima inasonta hartakai munhadu munga juna. Yanzu malan don Allah atemaka man da shawara yadda zamuyi lbr da ita nasoyayya wanda musulunci ya yarda dashi, dakuma hanyoyin da zanbi domin inga taqara sona, ni bantaba soyayyaba malam sai akanta. Don Allah ayiman wannan temako nagode Allah yaqara bada ilimi mai albarka

           *_AMSA_*

 Wa Alaikum Assalam Wa Ramatullahi Wa Barkatuhu:-

Zaka sami wani da ka sani a wannan Garin da yarinya take, ya yi maka Binciken Dabi'arta da ta Iyayenta. Sabida Ba'a Aure sai Da Bincike. Duk Auren da Akayi babu Bincike Akwai Matsala.

 Daga nan kuma sai ka tura Iyayenka bayan ka Amintu da Tarbiyyarta da Ta Yan Gidansu. Kaima Kuma Ka Basu dama Su zo Garinku Suyi Bincike akanka. Addinin ka ds Kuma Yaya dabi'unka suke? Ya Kamata Mutane suke ganewa. Akwai Banbanci Tsakanin addini da kuma Dabi'a ko ince da halayya ko kuma Ince yadda ka Iya Mu'amula. Wani Namijin yana da Addini, Amma bai Iya Mu'amulantar Mutane ba. Idan ya zo Neman Auren Diyarki ba zaku gane hakan ba. Sabida Nema ya zo yi.

 Zai boye duk wani Halayyar sa Maras kyau, ya Bayyana Kyawawan. Da zarar Anyi Aure, sai Abubuwa su Chanja su Rikirkice. Sai ya zama kamar ba Wanda Kuka sani ba.

 Shiyasa Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasallam Yace DUK WANDA YA ZO NEMAN AUREN DIYARKU, IDAN KUN GAMSU DA DABI'UNSA DA ADDININSA, SAI KU AURAR MASA.
 Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasallam Yace a Bincika Dabi'u.

 Domin Nagartacciyar Dabi'ah ce take zaunar da Aure. Akasin Hakan Kuma yana Lalata Aure. Sabida haka Kaima kq bq su dama su Bincikeka Daidai Gwargwadon yadda zasu Iya gamsuwa da kai su Baka Aure.

Allah shine Masani.
Post a Comment (0)