SHIN YA DACE MACE TA FADAWA NAMIJI CEWA TANA SON SHI?
*TAMBAYA*❓
Salam, Allah ya kara taimakon malam tambayata anan itace;
Wata mace ce take son wani mutun amma shi baisan tana son shi ba, kuma har takai ga tana kore mazajen da suke zuwa nemanta da aure.
To shin akwai laifi gareta don ta Kore wadancan, kuma ko ya dace ta fadama wancan wanda take so cewa tana son shi?
Wassalamu alaikum.
*AMSA*👇
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu
Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalam ala rasulillah.
Ita dai soyayya Allah ne ke jefa ta a zukatan bayi, amma a al'adar mu nan ba'a saba ganin mace tace da namiji tana son shi da aure ba, hakan yayi sanadiyar matan mu sun yi asara ko rasa mazaje na gari da yawan gaske.
Saboda haka idan bata fadi mashi tana son shi ba, mai yiyuwa ba zai gane hakan ba, a haka kuma ta cuci kan ta ne kawai, amma babu laifi a kan ta, kamar yadda babu laifi a kan shi. Shawara a nan ita ce, idan ta yadda da hankalin shi da kuma wayewar shi, toh ya dace ta fada mashi cewa tana son shi da aure, amma da sharadin idan zata iya hakuri da duk amsar da zata biyo baya. Idan wacce ta dace da son zuciyar ta ne, falillahilhamdu wa ni'imah, amma idan kuma ta zamo akasin abinda take zato daga gare shi ne ma'ana bata dace da son ran ta ba, sai tayi hakuri ta fauwala ma Allah al'amarin.
Amma kore wadanda suke zuwa neman ta da aure, wannan bai dace ba, domin ya saba ma hankali da shara'a ma, kuma zai iya zama wauta ce ba karama ba. Domin Allah yace mai yiyuwa ku ki wani abu alhali shine alkhairi gare ku, kuma mai yiyuwa ku so wani abu alhali shine sharri gare ku, Allah ne yake sanin (inda alkhairi da sharri) ku baku sani ba.
(... وَعَسَىٰۤ أَن تَكۡرَهُوا۟ شَیۡـࣰٔا وَهُوَ خَیۡرࣱ لَّكُمۡۖ وَعَسَىٰۤ أَن تُحِبُّوا۟ شَیۡـࣰٔا وَهُوَ شَرࣱّ لَّكُمۡۚ وَٱللَّهُ یَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ)
[Surah Al-Baqarah 216]
Abinda yafi dacewa shine ta amsa ma wanda ya kwanta mata a rai, tayi istikhara tana mai rokon Allah ya zaba mata mafi alkhairi tsakanin wannan da yazo da wancan da bai san ana yi ba.
Shawara a nan ita ce kar ta sake korar wanda yazo da niyyar auren ta, don yin hakan, shine sakin na hannu kamun na dawa. Ba wani dalili (na shara'a ko na hankali) da zai sa ta kore su.
Ina rokon Allah ya baki wanda kike so idan alkhairi ne gare ki, kuma shi ma ya bashi ke idan yana son ki kuma alkhairi ce gare shi duniya da lahira.
Wallahu ta'ala a'lam.
*_Amsawa_* :
*Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248