BASHI DA KUƊI, SHIN ZAI IYA CIN BASHI DAN YA YI LAYYA??.
Shaykh Uthaymeen (Rahimahullah) yace;"Idan har mutum ya tabbatar cewa idan ya ci bashi zai iya biya alokacin da yayi alkawarin biya din, kamar misali ya kasance ma'aikacine gashi kuma layya ta zo alokacin da babu kudi a wurin sa, amma yana da tabbacin karshen wata zai karbi salary sa ya biya to anan babu laifi yaci bashi ya saya abun layyan ko kuma ya karbi dabbbar layyar bashi.
Amma kuma idan yasan bazai iya cika alkawari ba saboda bashi da wata tabbatacciyar hanya da kudin zasu zo masa to anan baya halasta yaci bashi yace zai yi layya, domin idan yaci bashi zimmarsa ta shagaltu da abunda Allah bai Dora masa ba.
اللقاء الشهري..
#Zaurenfisabilillah
Telegram :
https://t.me/Fisabilillaaah
Facebook:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/