FALALAR KWANAKI GOMAN FARKON WATAN ZUL HIJJA 03



_*FALALAR KWANAKI GOMAN FARKON WATAN*_
                        _*ZUL-HIJJA*_
                    

                  _*DARASI NA UKU*_

  _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

    _*ABUBUWAN DA AKESON AIKATAWA A*_
            _*WAƊANNAN KWANAKI*_

_Kamar Yanda Muka Sani Wannan Wata na Zul-Hijjah Wata ne da Ubangiji Yake Ruɓanya Lada Idan Mutum Yayi Aikin Alkhairi. Saboda Hakane Aka Kwaɗaitar Dayin Wasu Ayyuka Don Samun Gwaggwaɓan Lada. Ayyukan da Ake Buƙatar Mutum Ya Yawaita Aikatasu Sun Haɗa da:_

_*1. SALLAH:* Sallah Tana Daga Cikin Mafiya Ayyukan da Bawa Ke Samun Kusancin Ubangiji da Ita. Saboda Hakane Akeson Baya ya Dage da Aikata Nafiloli don Dacewa da Wannan Gwaggwaɓar Ladan. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

عن ثوبان رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: *{عليك بكثرة السجود لله فإنّك لا تسجد لله سجدة إلاّ رفعك إليه بها درجة، وحط عنك بها خطيئة}*
 (رواه مسلم)

_An Karɓo Daga Thauban (ra) Yace: Naji *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa: *“Ina Horonka da Yawan Sujjadah Ga Allah, Domin Bazakayi Sujjadah Ɗaya Ga Allah ba, Face Ya Ɗaukaka Darajarka Gareshi. Kuma Ya Kankare Zunubanka da Ita".*_
_(Muslim Ya Ruwaitoshi)_

_*2. AZUMI:* Azumi Yana Daga Cikin Ayyuka Masu Falala da Ake Buƙatar Bawa Ya Dage da Yinsu Cikin Waɗannan Kwanaki Goma na Zul-Hijjah. *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa a Cikin Ingantaccen Hadisinsa:_

عن هنبدة بن خالد عن امرأته عن بعض أزواج النبي صلى الله عليه وسلم قالت *:{كان النبي صلى الله عليه وسلم يصوم تسع ذي الحجة، ويوم عاشوراء، وثلاثة أيّام من كل شهر}*
(رواه أحمد)

_An Karɓo Daga Hinbadah bn Khalid Daga Matarsa Daga Wasu Cikin Matan Annabi (ﷺ) Tace: *“Manzon Allah (ﷺ) Ya Kasance Yana Azumtar Kwanaki Tara Na Watan Zul-Hijjah, da Ranar Ashura, Da Kuma Kwanaki Uku na Kowane Wata".*_
_(Ahmad Ya Ruwaitoshi)_

_Imam Nawayi (ra) Yana Cewa: *“Azumtar Kwanaki Goma Na Zul-Hijjah Mustahabbi ne Mai tsanani".*_

_*3. YIN KABBARORI DA HAILALA DA HAMDALA:* Mustahabbi ne Yawaita Faɗin *“ALLAHU AKBAR, LA'ILAHA ILLALLAH, ALHAMDULILLAH"* A Cikin Waɗannan Kwanaki Goman Farkon Na Zul-Hijjah. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

عن ابن عمر رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلي الله عليه وسلم: *{فأكثروا من التهليل والتكبير والتحميد}*

_An Karɓo Daga Ibn Umar (ra) Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Ku Yawaita Yin Hailala da Kabbara da Kuma Hamdala".*_

وقال الإمام البخاري رحمه الله: *"كان ابن عمر وأبو هريرة رضي الله عنهما يخرجان إلى السوق في أيّام العشر يكبران ويكبر النّاس بتكبيرهما"*

_Imam Bukhari Yana Cewa: “Ibn Umar da Abi-Hurairah Sun Kasance Suna Fita Kasuwa a Cikin Kwanaki Goman Zul-Hijjah Suna Kabbara, Mutane Kuma Sunayin Kabbara da Kabbaransu"._

              _*SIGOGIN KABBARAR*_
_Hadisai Masu Yawa Sunzo Game da Sigar Kabbarorin da Akeyi a Waɗannan Kwanakin. Kaɗan Daga Cikin Sigogin Sun Haɗa da:_

*١- الله أكبر، الله أكبر، الله أكبر كبيرًا*

_*“ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR KABIRAN"*_

*٢- الله أكبر، الله أكبر، لا إله إلاّ الله، والله أكبر، والله أكبر، ولله الحمد*

_*“ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LÃ'ILAHA ILLALLÃH, WALLAHU AKBAR, WALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD".*_

*٣- الله أكبر، الله أكبر، الله أكبر، لا إله إلاّ الله، والله أكبر، الله أكبر، ولله الحمد*

_*“ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LÃ'ILAHA ILLALLAH, WALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD"*_

_*4. AZUMTAR YININ ARFA:* Yinin Arfa Yana Daga Cikin Yinin da Ubangiji Yake Matuƙar So Tare da Alfahari Dashi. Azumtar Wannan Yini Yanada Matuƙar Falala, Domin Ubangiji Yana Kankare Zunuban Shekaru Biyu Sanadin azumtar Wannan Rana. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yana Cewa Yayin da Aka Tambayeshi Game da Azumtar Yinin Arfa, Sai Yace:_

*{أحتسب على الله أن يكفر السنة التي قبله والسنة التي بعده}*
(رواه مسلم)

_*“Ina Kyautata Zaton Ubangiji Zai Gafarta Zunuban Shekarar da Tagabata da Shekarar da Zatazo".*_
_(Muslim Ya Ruwaitoshi)_

_*YA ALLAH KA BAMU IKON AIKATA AYYUKAN ALKHAIRI A WAƊANNAN KWANAKI MASU ALBARKA*_

_Ana Zan Dakata, Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba_
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)