WAI ANCE BA DOLE SAI AN JIKA KAI DUKA BA YAYIN WANKAN TSARKI...???



_Tambaya ta (379)_
....
. WAI ANCE BA DOLE SAI AN JIKA KAI DUKA BA YAYIN WANKAN TSARKI...???

_Assalamu Alaikum malam ance wankan tsari ba dole sai anjika kai duka ba indai wani bangare ya samu ruwa shikenn malam inason karin bayani Wasu kuma masu suma da yawa samn kai suna cewa jika kan na kawo musu matsala_
.
_
::
*_AMSA:-_*
_waalaikumussalamu To wannan maganar Gaskiya bata da tushe balle makama Domin A zahirin hadisan da sukazo game da wankan tsarki dukkansu suna nuni ne da game jiki baki daya To kinga idan akace game jiki baki dayansa kenan ashe wajib ne wanke kai baki dayansa yayin wankan tsarki, Sabida haka Maganar cewa ba dole sai an jika kai baki dayansa yayin wanka ba Wannan shaci faďine kawai, Domin hatta kitson dake kan mace wasu malaman cewa sukayi sai ta warwareshi domin ruwa ya samu damar ratsa dukkan gashin baki dayansa Musamman idan wankan daukewar haila ko na Biki zatayi. Amma kamar wankan janaba shi basai ta kwance gashin kanta ba sai dai wajib ne ta tabbatar ruwan ya ratsa dukkan gashin nata._
.
_Inda kawai aka samu sabanin fahimtar wasu daga cikin magabata shine a babin shafar kai yayin al'wala Wasu daga cikin magabata Allah yayi musu rahama suna ganin ba dole sai mutum ya shafa kansa baki daya ba idan ya shafa wani bangaren na gashin kansa ya wadatar Wannan shine fahimtar Imamu Abu Hanifa Allah yayi masa rahama To Amma koda wannan fahimtar tasa ta sabawa Fahimtar mafi yawan magabata Wannan yasa shima baza'ayi Amfani da wannan fahimtar tasa ba, To kunga kenan idan Har yayin Al'wala bazai yiwu kayi shafar kai a iya wani ďan bangare na gashinka ba To kuma taya za'ace a wankan tsarki ba dole sai ka game duka gashin kanka da ruwa ba??? Sabida haka Jika dukkan gashin kai da ruwa yayin Wankan tsarki wajib ne kuma Duk wanda ruwan bai ratsa dukkan gashinsa ba ma'ana be game dukkan gashin kan da ruwa ba To wankansa bai cika ba._
.
_Dangane da cewa jika kai yana kawo matsala to idan sun tashi yin wankan bayan sun wanke hannayensu sau ukun Su tsoma hannunsu cikin ruwan sai su duddurza gashin kan nasu kamar yadda Annabiﷺ ya kasance yana yin hakan, kuma bincike yana nuna cewa duddurza gashin yana tushe kafofin kashin kan wanda dazarar mutum ya kwara ruwa akan nasa wanke kan bazai haddasa masa ciwon kai ba_****
..
_Wallahu A'alam_

_ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ_
_idan Anga Gyara A Sanar Damu  👏_
=
_Na So Kun San Tarin Lada Da Albarka Da Ake Samu Ta Hanyar Yada Ilimi  Ko Wani Alkhairi_
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)