FITAR MATA ZUWA SALLAR IDI 01



FITAR MATA ZUWA SALLAR IDI 🕌🚶🏿‍♀

*001*

Daga Ummu Adiyya, yardar Allah ta tabbata a gare ta, ta ce: “Manzon Allah (ﷺ) ya umarce mu da cewa 'yanmata waďanda suka isa aure, da masu haila, da killatattun 'yanmata duk su fita don su halarci idin karamar sallah da babbar sallah. Masu haila su 'kaurace wa masallacin idin; amma dukkansu su halarci alheri da addu'ar musulmi.” Malamai shida suka ruwaito shi. 
.

Al-Shaukani ya ce:

Wannan hadisin da wasu hadisan masu irin wannan ma'ana duk sun nuna halascin fitar mata zuwa masallacin idi, ba tare da bambanci ba tsakanin budurwa, da bazawara, da yarinya, da tsohuwa, da mai haila da waninta, ban da mai yin idda, ko kuma wacce akwai fitina a cikin fitarta, ko kuma mai wani uzuri. (Duba 3/306).
.

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyya, Allah Ya ji qansa, ya ce a cikin _Majmu'ul Fatawa_ (6/458-459):

Annabi (ﷺ) ya gaya wa muminai mata cewa sallarsu a gida ta fi masu falala a kan zuwa sallar juma'a da sallar jam'i, ban da sallar idi. Ita kam ya umarce su da su fita don su halarce ta. Wannan kuwa a zahiri, kuma Allah ne mafi sani, saboda wasu dalilai ne kamar haka:

Na farko, wannan sallah sau biyu ce kawai a shekara, don haka sai aka yardar masu, sabanin sallar juma'a da sallar jam'i.

Na biyu, sallar idi ba ta da sallar da take tsayuwa a matsayinta, sa6anin sallar juma'a da sallar jam'i; domin kuwa idan mace ta yi sallar azahar a ďakinta, wannan ce juma'arta. 

Na uku, sallar idi fita ake yi wajen gari don ambaton Allah, don haka tana kama da aikin hajji ta wasu fuskokin. Shi ya sa ma idin babbar sallah a lokacin hajji ya zamanto shi ne idin da ya fi kowanne girma ga alhazai. 
.

Zan dakata a nan, za mu ci gaba in shā Allah. 
.

*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
(Ansar).

*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*

Telegram: https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)