BAITUKAN TITSIYE



BAITUKAN TITSIYE 
 
1.
Har ga Allah ya ga canji, 
'yan maza sun ba shi 'kwanji, 
don kunun yau ya yi yaji, 
ga shi har ya yo gudaji, 
gaske ne ba wai dabo ba. 

2.
Yanzu kam an jijjiga shi, 
babu shakka an 'kure shi, 
yai li6is har ya yi laushi, 
tun azal waye ya sa shi
yin fad'an da ba zai iya ba? 

3.
Yau a filin nan na taro, 
tun haraba yai ta 'kwauro, 
yai alamun nan na tsoro, 
kan mazaje na su hauro, 
mun yi galba bai sani ba.

4.
Mun ga jaki yau da kaya, 
sai ka ce ya harba 'kwaya, 
mai tulin matsala na kwanya, 
mai buhun roka na 'karya, 
shi fa bai san bai sani ba. 

5.
Shi kad'ai sai share fuska, 
ga shi A.C na gaban ka, 
winduna na bada iska, 
don kawai an gagare ka, 
Ka yi shargab ba da wai ba. 

6.
Yau mutan kogo da cikas, 
sun yi tsit duk sun yi mankas, 
don sadaukin ya yi yo 'kas
an yi mar taunar 'kashi 'kas, 
sai ka ce ba shi ba ne ba. 

7.
Ma su posting babu posting 
yau fa paging babu casting, 
na tsaya fa ina ta waiting, 
wai ashe yau babu acting, 
jarumin ne bai fito ba. 

8.
Sun 'ki posting sun 'ki motsi, 
sun 'ki jifa ko da dutsi, 
mai gidan yau ya ji santsi, 
shafukan yau sun yi watsi, 
duk da su ba su ankare ba. 

9.
Kai kanawa kun biyani, 
don ko yau an fidda raini, 
har ga Allah kun tsuma ni, 
dole ne in yo bayani, 
kauce-kauce fa ban iya ba. 

10.
Godiya gun shugaban ku, 
dakta Abdullahi na ku, 
Baba Gandujen garin ku, 
Khadiimul islamu na ku, 
Baba ba mutakabbiri ba. 

11.
Baba mai imposibili
kai Kad'ai ka zam dalili, 
na ga yau ka tada balli, 
mun gani yau kam a fili, 
Ka yi aikin nan na duba. 

12.
Dakta Rabi'u ka biya ni,
kai ka taka hawa na tsani, 
har ta kai ka kai ga tsauni, 
Ka hana shi ya yo sukuni,
in da ku fa ba zai sake ba. 

13.
Ga Haya'ki nan fa shi ma, 
Sheikh kabiru kana da himma, 
saurayi ne mai karama, 
shi ya mar mari 'kazama, 
bai raga mar ko kad'an ba. 

14.
Mai madattai ka yi komai, 
mai shiga ta irin imamai, 
Ka yi bulalai kazamai, 
don ko har ka 'kara mai-mai, 
ba da wasa yau ka zo ba. 

15.
Shehu Mas'ud jarumi ne, 
don ko shehin d'an gari ne, 
maganin 'ya'yan tsiya ne, 
shi ya kwashe 'kafar ya danne, 
ko kad'an bai tausaya ba. 

16.
Shi ko farfesan ga shehu, 
kamili ne bai da ihu, 
shi ya sanya ruwan a murhu, 
ya fa san ta'adil da jarhu, 
adali ka ke wallah Baba. 

17.
Rabbi Allah kare sunnah, 
'kara tozartar da sauna, 
sa idan yara 'kanana, 
sun ka gan shi kawai su nuna, 
duk fishin su fa ba da wai ba. 

18.
Ni fa Ahmadu nai salati, 
ga shi har na tsara baiti, 
yau 'kiraza sun yi saiti, 
lunguna sa'ko da titi, 
ban ji wanda su ke musu ba. 

✍️ Ahmad Usman El-nafaty 
     10/7/2021
Post a Comment (0)