GOMAN FARKO NA ZUL HIJJAH.

GOMAN FARKO NA ZUL HIJJAH.



 1- Yazo cikin sahihul bukhari hadisin Abdullahi Dan Umar cewa Annabi s.a.w. yace:" Babu wasu kwanaki da aiki nagari yafi soyuwa zuwa ga Allah fiye da wadannan kwanaki goman-yana nufin goman zulhijjah- sai sukace: koda jihadi fisabilillah? Yace: Koda jihadi fisabilillah sai dai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai ba."

2- lalle kwanaki ne masu mutukar daraja saboda darajarsu ne ma Allah s.w.t. da kansa yai rantsuwa dasu a cikin a farkon suratul fajri saboda ya nuna Mana girmansu da falalarsu.

3-an tambayi shaikhul Islam cewa da goman farko na zul hijjah da goman karshe na Ramadan wadanne sukafi falala? Sai yace idan ta fuskar yininnika ne to goman farkon zulhijjah sunfi,idan kuma ta fuskar darare ne to goman karshe na ramadana sunfi. Duba fatawal kubra juz'i na 2 shafi na 477.

4- ayyukan alkhairi sun hada da yawan ambaton Allah. Yazo cikin musnad na Ahmad daga Dan Umar r.a. cewa: Annabi s.a.w. yace:"babu wasu kwanaki da suka fi girma a wajen Allah ko sukafi soyuwa awajensa daga aiki a cikinsu fiye da wadannan kwanakin goma,Don haka ku yawaita hailala da kabbara da hamdala a cikinsu".

5-daga cikin ayyukan alkhairi akwai karatu alkur'ani da tadabburi a cikinsa.don haka Dan uwa ka dage ta karatun alkur'ani a cikinsu.

6- ya kunshi sada zumanta da taimakon yan'uwa yazo a cikin hadisi cewa"duk Wanda yake so a yalwata Masa cikin arzikinsa kuma a tsawaita Masa cikin shekarunsa to ya sada zumuntar sa."

7-azumi yana daga cikin ayyukan nagari masu falala da mutum zai ribata a wadannan kwanakin guda tara, idan bai azumce su duka ba to kada ya Bari azumin arfa ranar Tara ga wata ya wuce shi Domin Yana kankare zunubin shekara biyu Kamar yadda yazo a Muslim hadisin abiy qatadah.

8-sadaka:ta wajibi (zakka) ko ta nafila suna daga cikin ayyuka nagari da zaka ribata a wadannan kwanakin yazo cikin hadisi cewa:"kaji tsoron wuta Koda ta tsagin dibino ne, idan baka samu ba to Koda ta daddadar kalma ce"

9-aikin alkhairi ya kunshi duk abinda Allah yake so kuma ya yarda dashi to kayi iya yinka kaga ka yawaita shi a wadannan kwanakin.

10- ya Dan uwa Wanda ka sakaci a ramadanan ka ga dama ta samu, yau ake gobe sai labari, Don haka kada ka Bari wadannan gwala-gwale kwanakin su wuce ka ba tare da ka hanaka asusunka na lahira ba.

Allah yasa mu dace. Amin

Abu awanatal kanawiy@
29-11-1441 hijriyyah
Post a Comment (0)