HAJIYA MAIRO MAI TONON SILILI



HAJIYA MERO MAI TONON SILILI..!
Awata kotu ne ana sauraron kara, jama’a sun cika makil, sai alkali ya bukaci wata tsohuwa ta fito donin bayar da shaidar wanda ya kawo kara an sace masa mota. Da tsohuwa ta fito, sai lauyan wanda yakawo kara ya fito domin yima tsohuwa tambayoyi kamar haka:
Lauya: Baaba shin ko zaki iya gayawa kotu sunanki?
Tsohuwa tace, “Ni sunana HAJIYA MERO MAI TONON SILILI.
Lauya ya sake tambayarta ko HAJIYA MERO MAI SILILI kinsan ni waye?
Tsohuwa ta gyara tsayuwarta, sannan tace ” Eh mana nasan ka ai tun kana karaminka, kai makaryaci ne, ka iya hada waje, gaka da yaudara da kuma rashin iya magana, ga gulma da kuma shaye shaye da neman mata.
Lauya jikinsa yayi sanyi cikin alamun jin kunya yaje kusa da abokin aikinsa, wato daya lauya sai ya cewa tsohuwar “Baaba wannan fa ko kinsan shi?
Tsohuwa ta gyara mayafin dake rataye akafadunta tace, 

Toh ai gyara kaima akan wannan domin, wannan kam ai asalin cikakken dakiki ne gashi da shegen son jin gulma ga kuma muna furci, kai bari kaji yanzu haka yana cin amanar matarsa da wasu matan banza guda uku kuma daya daga cikinsu ma matarka ce Lantana”.
Tana rufe baki sai alkalin kotun wanda tunda aka fara shari’ar baice komai ba, yana sauraron wannan tsohuwar yadda take fede biri har wutsiya.
Sai alkali ya kira dukkanin lauyoyin 2 cikin murya kasa kasa yace, “kunsan Allah duk shegen daya kuskura ya tambayi wannan tsohuwar ko ta sanni tabbas zaici ubansa kuma sai nasa an kwace masa lasisinsa na aiki…
HAHAHHAHAHAHHAHAHAH!!!
Nima duk wanda ya tambayeni sai na Goge wannan application din daga wayar sa HAHAHAH 
Post a Comment (0)