HUKUNCE HUKUNCEN IDI BIYU DAKUMA LAYYA:



HUKUNCE HUKUNCEN IDI BIYU DAKUMA LAYYA:
=
.
*DAGA ZAUREN*
*KITABU WAS SUNNAH*
=
*مجلس تعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
+2348036222795
+2349031200070
=
=
 Yau 01-12-1439
        11-08-2018
Cigaba da karatun littafi mesuna _*أحكلم العيدين و الأضحية*_
_*HUKUNCE HUKUNCEN IDI BIYU DAKUMA LAYYA:*_
=
=
Wallafar Malam Abubakar binu Amin Al-anchawi Kaduna
=
Darasi na biyu:
=
_*1---IDI DAKUMA HIKIMAR SHAR'ANTATA:*_
°
_1----Idi dai iri biyu ne, akwai idi na buda baki bayan kammala azumin watan ramadan, dakuma idin layya bayan watan zulhijja yacika kwanaki goma*****_
_2-----Hakika anshar'anta idi, domin musulmai su bayyana farin ciki da walwala, da godiya akan ni'imomin Allah da shiriyarsa, ta hanyar raya wata shara'a daga cikin shari'o'in musulinci*****_
=
_*2---SHAR'ANTUWAR SALLAR IDI:*_
°
_3----Sallar idi abar shar'antawace da littafin Allah da sunnah, da haduwar kai na malaman farko, ita sunnace ta wajibi, hakika Annabi (s.a.w) da sahabbansa sun nace akanta, hakama musulmai wadanda suka biyo bayansu nafarkonsu da 'yan baya****_
_4-----Yana zama wajibi akan mutane sufita zuwa filin ida baki daya, kai Annabi (s.a.w) ya umarci mata wadanda suke haila cewa su nisanci filin idin****_
_5----Lokacin sallar idi yana kamawa idan rana ta daga kadan, kuma yana wanzuwa har kusada daidaituwan rana****_
_6----Sunnah shine asallaci sallar idi a sarari can bayan gari, amma tana halasta ayi a masallaci in akwai hanzari, kamar ruwan sama ko maqiya da sauransu****_
=
=
Zamu dakata anan sai kuma fitowa tagaba idan Allah yaso
=
=
Allah yasa mudace,
.
.
✍🏽
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_*(ABU ZULAIKHA)*_
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)