HUKUNCIN CIN ABINCI TARE DA KAFIRAI



HUKUNCIN CIN ABINCI TARE DA KAFIRAI :
TAMBAYA TA 2314
*******************
Assalamu alaikum malam. Ina mai fatan kuna cikin koshin lafiya.
Tambaya ta shine mutun ne ya kasance yana aiki tare da arna, wajen aikinsa tare da arna ne yeke aiki agidan ma'aikata.
To sai dai idan an kawo abunci ana ci tare. Yaya wannan matsala yake?. Malam Allah ya kara maka lfy.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Idan abincin bai kunshi wasu hatamtattun abubuwa ba (Kamar giya, Naman kare, ko naman alade) Kuma su basu da tsananin Qiyayya ko Qokarin tada hankalin Musulmai, to ya halatta kaci abinci tare dasu tunda awajen aiki ne kawai, ba wai ko yaushe ba.
Akwai hadisi wanda Sayyiduna Anas bn Malik (ra) ya ruwaito cewa wani Bayahude ya gayyaci Annabi (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) zuwa gidansa domin suci abinci (Gurasar Alkama da Miya) Kuma Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya amsa gayyatar yaje sunci abincin.
(Aduba Almughnee na Ibnu Qudaamah juzu'i na 7 shafi na 3).
Sannan akwai hadisin da Imamu Muslim ya ruwaito daga Sayyiduna Abu Hurairah (Radhiyallahu anhu) cewa Manzon Allah (saww) ya kira wani kafiri zuwa gidansa kuma ya ciyar dashi abinci. Wato yasa an tatso masa nonon Akuya, kafirin ya shanye. Ana tatsowa yana shanyewa har sai da ya shanye Nonon awakai guda bakwai.
(Sahihu Muslim hadisi na 2063).
Ya halatta kaci tare dasu amma kada ka mayar dashi al'adarka ta yau da kullum.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (31-08-2017 09-12-1438).
Post a Comment (0)