HUKUNCIN MATAR DAKE FITA BA TARE DA IZININ MIJINTA BA



HUKUNCIN MATAR DAKE FITA BA TARE DA IZININ MIJINTA BA :
TAMBAYA TA 2793
*******************
Assalamu Alaikum
Allah yakarawa mallam ilimi da imani yakuma saka da gidan Aljannatul firdaus
Menene hukuncin macen da take yawan fita agidan mijinta koda saninsa ko bada saninsa ba?
Menene kuma dalilai daze sa mace tafita agidan bissa karantawar sunnar annabi (saww) ?
Wassalam
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Haramun ne mace ta fita daga gidan mijinta ba tare da izininsa ba. Allah madaukakin sarki ya gaya wa matayen Manzon Allah ﷺ tare sauran matayen muminai "KU ZAUNA A GIDAJENKU KADA KU FITA (TARE DA BAYYANAR DA ADO) IRIN FITAR NAN TA JAHILAN FARKO".
Sannan koda matar da aka saketa, musulunci bai yarda a barta ta rika fita taje inda taga dama ba. Acikin Suratut Talaq da suratun Nisa'i da suratul Baqarah da sauran wurare Allah Madaukakin Sarki ya fa'di yadda ake yin iddar saki da iddar rasuwa, da sauransu.
Imamul Qurtubiy yace "idan har bukata ta sanya za'a fita din, to lallai ne fitar ta kasance cikin kulawa tare da cikakkrn suturce jiki".
Tabbas duk matar dake fita ba tare da izinin mijinta ba, fushin Allah yana samunta har sai ta dawo ta nemi yafewarsa.
Daga cikin manyan dalilan da zasu iya jawo fitar mace daga gudan mijinta akwai :
1. Neman ilimin addini - idan har mijinta bashi da ilimin da zai koya nata ibadah, kuma ba zai iya dauko wata macen da zata koyar da ita a gida ba, Kuma shi kansa bashi da malamin da zai koyar dashi sannan ya dawo ya koyar da iyalinsa da kansa.
Kuma wajibi ne koyon ilimi ya zamanto awajen mace 'yar uwarta zata koya. Idan kuma duk garin babu matar dake da ilimin da zata koya awajenta, shikenan sai mataye da yawa su taru awaje daya sannan a nemo namiji mai ilimi, mai tsoron Allah wanda zai karantar dasu ba tare da sun ganshi ko shi ya gansu ba. (wato a sanya labule atsakaninshi dasu).
2. NEMAN LAFIYA : Idan bata da lafiya ya halatta ta fita zuwa asibiti domin ganin likita.
3. ZUMUNCI : Ya halatta ta rika zuwa tana gaida mahaifanta ko makusantanta (kamar Qannai ko yayun iyayenta) idan bukatar hakan ta taso. Wannan ya ha'da har da ta'aziyyah da duba marar lafiya.
4. BAYAR DA SHAIDA : Idan wani abu ya faru wanda ake bukatar matar taje ta bayar da shaida a gaban alkali ko wata hukuma.
5. SANA'A : Ya halatta ta fita taje tayi sana'a idan har mijinta ba zai iya daukar nauyinta ba, Kuma bata da wani wanda zai taimaka mata. Amma wajibi ne sana'ar ta zamto halastacciya kuma babu chudanya ko kebancewa da mazaje acikinta.
6. FITA DOMIN HALARTAR SALLAH : Yana zama halal idan har zasu fita bisa cikakken lullubi tare da rashin kebancewa ko chudanya da maza. Ya halatta su halarci sallar Eidi ko Jumu'ah, har sallolin farilla a masallaci amma akwai Qarin wasu Qa'idodi da malamai suka ajiye.
Amma fita don yin cefane ko kaiwa yara makaranta, wannan hakkin namiji ne. Bai halasta mace ta fita musamman domin yinsu ba, sai dai bisa larurar rashin miji, ko wani Muharrami wanda zai isar mata.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (16/12/1441 06/08/2020)
Post a Comment (0)