HUKUNCIN MA'AURATAN DA SUKA CI GABA DA ZAMA BAYAN SAKI UKU :
TAMBAYA TA 2156
****************
Assalamu Alaikum warahmatullah wabarakatuhu
Malan barkanmu da warhaka
ga tambaya dftn za'a duba mana wannan al'amari Allah yaqara jagoranci wato Malan:
-Mauratane guda biyu wani al'amari ya afku akansu shekaru 25 baya :
Dafarko an đaura mussu Aure matar bata tare ba sai aka samu sa6ani na iyaye sai mijin yace ya saketa saki đaya.
Bayan wani lokacin sai aka samu dai-daituwa sai Aka sake sabon wani đaurin Aure sunci gaba da rayuwar su harda Zuri'a.
Na biyu sunata rayuwa lokaci nata turawa sai suketa samun sa6ani sai mijin wata rana ya rubutu saki ta hanyar rubutu a takadda sai matar tađauka tagani sai tabawa Yayar mijin sai ta yaga tace shirme ne ba inda matar zata je, sakin ma be yiwu ba sai suka cigaba da zamansu da qarin Zuri'a.
Na uku sunata rayuwarsu sai mijin yaje yayo sabon Aure sukaci gaba da zama tare sai watarana aka samu sa6ani matan suna husuma sai mijin yace suje dik yayi mussu saki uku uku.
Bayan wani lokutan tsahon watanni ita Matar ( tabiyun). Amaryar tafita taje tasake wani Auren.
Ita kuma Uwargidan sai yazo yace Aurensu be qare ba yayi tambaya waje-waje ance akwai kome sai suka koma aka maida Aure yanzu shekara goma kenan da qarin Zuri'a kuma.
Tambayar anan itace Malan bayan dikkan wannan bayanai Auren yana nan ko yaya abin yake ya kuma matsayin Zuri'ar ?.
AMSA
***
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Gaskiya wannan aurensu ya riga ya Qare tun lokacin da yayi saki ukun nan.
Sakin da yayi na farko din nan ya yiwu. Sai kuma wancan na biyun wanda ya rubuta a takarda, shima ya yiwu tunda har ta gani da idonta. Ita kuwa yayar mijin ai ba a hannunta igiyar auren take ba. Kuma shi saki ba'a warwareshi bayan ya riga ya afku.
Sannan daga Qarshe bayan ya Qaro aure yayi musu saku uku uku ita da amaryar. Shikenan a nata bangaren dama akwai saki biyu tuntuni. Don haka yanzu kalmar saki ta zama biyar kenan atsakaninsu. Sai adauki guda daya daga cikin wadannan ukun adora akan biyun farkon chan. Shikenan ya zama saki uku.
Babu wata hujjah a addinin Musulunci wacce za'a dogara da ita amayar da irin wannan auren wanda akayi saki uku alokuta daban daban. Kuma bisa dukkan alamu bai tambayi Maluman da suka san ilimin addini bane. Ko kuma dai yayi amfani da son ransa ne kawai.
Wannan zaman nasu ba za'a kirashi da sunan "Aure" ba. Don haka suji tsoron Allah su gaggauta rabuwa taje tayi iddah tayi wani sabon aure kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Su kuwa iyayen suci gaba da tuba zuwa ga Allah bisa wannan mummunan laifin da suka aikata. Idan son rai suka bi, to zama ya Zaman zina kenan sukayi. Kuma babu gado tsakanin Uban da wadannan yaran da aka haifa bayan saki ukun.
Idan kuma Ijtihadi sukayi bisa kuskure, shi kansa ko kuma Malamin da ya bashi fatawar, to al'amarinsu yana ga Allah. Amma dai suci gaba da neman gafara da tuba ga Allah (swt).
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (09-04-2017).
