KU KAUDA KANKU DAGA KALLON LAIFUKAN MAZAJENKU NA AURE.



KU KAUDA KANKU DAGA KALLON LAIFUKAN MAZAJENKU NA AURE.

Mun tsinci kanmu awani zamani wanda kullum ma'aurata (musamman matan aure) kamar jira suke mazajensu su aikata wani kuskure.. Nan da nan sai ta rubuto laifukan mijinta ko laifukan Uwar mijinta ta tura group din Qawayenta na Whatsapp. 

Daga nan kuma za'a yi kwana biyu ko uku ana ta rubuto ra'ayoyi kala-Kala. Tun daga kan masu tsine wa mijin, har zuwa masu bata shawara ta gari.. 

Babban munin abun ma shine akwai wasu matayen da sukan bude shafuka akan Platforms kamar facebook ko Instagram, wanda kusan kullum aikin kenan. 

Wasu lokutan abun yakan shafi kwanciyar aure, etc. Gashi kuma Manzon Allah ï·º yace duk namijin (ko macen) da zata biya bukatarta da mijinta, Ko mijin da zai biya bukatarsa da iyalinsa, sannan su fito suna watsa sirrinsu aduniya, t suna daga cikin mafiya shan tsananin azaba aranar lahira.. 

Binciken laifukan mutane mummunan laifi ne akan kansa. Ballantana kuma watsa ma duniya.. Ballantana abinda ya shafi zaman aure.. Ko sirrin mijinki, uban 'ya'yanki. 

Yake 'yar uwa ki sani Babu yadda za'ayi wata matar da ba Malama masaniyar Alqur'ani, Hadisi da Fiqhu da Ilmul Usool ta zama ita zata gaya miki yadda zaki zauna da mijinki.. 

Ba lallai ne ya zamto tafiki sanin addini ko aiki dashi ba, kuma shin me yasa ba zaki nemi shawarar daga malamarku ta Islamiyya ba?. Shin kin sanar da Mahaifiyarki ko wata mace mai hankali acikin danginki ne, duk basu baki shawara tagari ba? 

Babu wani namijin da ba ya yiwa matarsa laifi. Hatta mahaifinki yana yiwa mahaidiyarki laiifi. Amma hakuri tayi da halinsa kamar yadda shima yake hakuri da nata halayen. Wannan hakurin sgi ya janyo har aka haifeki dake da Qannenki ko yayunki. 

Umar bn Uthman Almakkiy (rah) yace : "Yana daga cikar mutuncin mutum ya zamto yana kauda kansa daga kallon laifukan mutane"

Al A'amash (rah) yace : "Kauda kai daga laifukan mutane yakan buche wutar sharruka masu yawa".

Al Imam Ibnul Jauzee (rah) yace "Kawar da kai daga kallon laifukan mutane bai gushe ba, yana daga mafiya daukakar halayen karamci"

Nasiha ce.. Wanda yaji haushi Allah bashi hakuri..Wacce taji haushi, Allah bata hakuri.. I come in peace. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (07/07/2021 27/11/1442).
Post a Comment (0)