KUNDIN MA'AURATA 02



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*💌KUNDIN MA'AURATA //02💞*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

*TASIRIN BAMBANCIN HALITTA A ZAMANTAKEWA*

Allah SW ya halicci namiji da mace ya kebe kowanne daga cikinsu da irin aikin da zai yi gwargwadon halittarsa, koda a ce maza suna zaluntar mata wurin killace su a cikin gida da hana su fita neman abin na kansu wanda hakan zai iya nuna cewa zalunci ne a sarari da mazan suke yi don nuna mamaya wurin yin amfani da qarfin da Allan ya ba su, amma da wani namijin zai tilasta matarsa ta riqa fita tun safe zuwa yamma don ta yi kafintanci, kanikanci ko leburanci ko tuqin mota a tasha don neman abin da za a ci a gida da sutura da sauran abin da gidan yake buqata, ko mazan ba su yi wa junansu magana ba, matan za su kira namijin da suna azzalumi, mara tausayi, mugu, domin ya daura wa matarsa abin da bai dace da ita ba, a nan ba tare da wata jayayya ba za a yi hukuncin cewa aikin da take yi ba nata ba ne, shi ya kamata ya fita ya nemo, nata sarrafawa ne kawai, ba inda aka ce su fita tare bare a sarayar mata da nauyin ciyar da gida, nan fa don aikin na wahala ne, ba a yi ma maganar wanda za a yi a bakin rai ba kamar sha'anin tsaro.

Shi kuwa namiji in ya sami wuri ya shantabe a gida ya zama bai neman na kansa, koda ya dauki nauyin shara da dafa abinci a lokacin da matarsa ta fita, ya hada da tarbiyar yaran da ta bar masa, ba za ka taba jin cewa musaya aka yi ba yanzu ita ce maigidar, ji za ka yi ana cewa "Duk abin da take yi taimaka masa take yi a sanadiyyar mutuwar zuciya da ya samu, shi ya sa ya yi watsi da wajibinsa, kuma za ta yi masa gori a duk lokacin da ta ga dama don saboda halin ko oho da ya yi da haqqin da yake kansa, ko kuma jin da za ta riqa yi na cewa tana bayar da dukiyarta kan abin da bai zama wajibi a kanta ba".

A Qur'ani dai wajen maganar Maryam AS babanta ya fadi cewa "Namiji ba kamar mace ba ne" wato ta wajen qarfi, jimiri da tsaro, ga abubuwan da suka shafi zuciya, wadanda suke da alaqa da saurin fushi, damuwa, sakaci da mantuwa, ko shagala, su ma in aka lura muhimman abubuwa ne da muke yawan samun sabani a kai, in ma ba a yi wasa ba duka da saki kan iya kurdadowa tsakaninsu, babban dalilin da ya sa mahaifammu in sun yi wa diyoyinsu qanana aure ba sa bari su yi nesa da su kenan, sukansa ido a duk ma'amalolinsu sai sun sami shekara tare da su suna cikin gandu, in sun tabbatar da za su iya riqe gidan kafin su sake su.

Abin da yake faruwa shi ne: Sau tari namijin yana so ne macen ta riqa gudanar da al'amuranta kamar yadda shi kansa yake, in ya gaya mata magana yana son ta aikata daidai ba tare da kuskure ba, kuma a lokacin da ya buqata, wanda hakan dabi'ar namiji ce, in har ba a sami abin da ya nema ba babu ko shakka za a sami rashin jituwa, wasu fada za su yi, wasu batanci, wasu ma har yakan kai ga bulala, ita kuwa macen tana buqatar maigidan ya riqa zama a gida, yana tarairayarta yana yi mata magana mai dadi, wannan shi ne galibin abin da matan suke buqata ba wai yawan jima'i ba, in har hakan ba ta samu ba, sai ka ga ana kai ruwa rana, ba za ta kula da qoqarin da mijin yake yi na kawo ababan masarufi ba, wadanda nemosu shi ne wajibinsa, ita tana kallon kasancewarsa a gida kawai, da sanyaya mata rai, cikin sauqi za ta ce aurensa bai da amfani, ko ta nemi fita.

Shi bai son kuskure, ita kuma ba ta son yawon da yake yi don kasuwanci, ko mauludin wani waliyi, ko wa'azin qasa wanda zai shafe kwanaki, komai dimbin amfanuwar da mutane za su yi da shi bai dame ta kamar cutuwar da take yi ita kadai ba, amma fahimtar kowa a dabi'arsa za ta rage manyan matsalolin da muke samu a aure, ita ta fahimci cewa shi namiji ne ta riqa yankan masa uzuri a kowani lokaci, shi kuma ya fahimci cewa ita mace ce rauninnan na matantaka yana tare da ita dole a yi haquri, sai ka ga an dade ba a sami rigima ba, galibin ma'auratan da ka ji su shuru sun fahimci junansu ne, ba wai babu sabani ne a tsakaninsu ba.

*QAUNAR BAKI BA TA ISA*

Tabbas qauna takan taimaka wajen tsare
Post a Comment (0)