HUKUNCIN YIN AIKIN GWAMNATI KO YIN KARATUN BOKO GA ÝA MACE A MUSULUNCI?
https://chat.whatsapp.com/BsuVPYdzZY7C1Sv0lgoNES
*TAMBAYA*❓
_Mlm sannu da kokari Allah yasaka muku da alkhairi, Mlm don Allah dama tambayata itace yin aikin gwamnati ko yin karatun boko ga yamace menene hukucinsa a addinin musulunci?_
*AMSA*👇
_To ýar uwa karatun boko ga ýa mace halal musamman fanninda yadace ace matane ke kulawa da ýan uwansu mata kamar likitanci d.s.s kuma musamman idan manufar yin karatun domin neman lahirane bawai neman duniya kaďai ba to wannan babu laifi mace tayi karatun bokon in sha Allahu._
..
_Dangane da aikin office kuma duk da cewa ita mace asali a shari'a zamanta a cikin gidanta shine mutuncinta wannan kuma ya shafi matar aure da wacce bata da aure kamar yadda yake ita kanta tafi samun kusanci ga mahaliccinta yayin da take zaune a cikin gidanta. Amma duk da haka babu laifi mace tana iya fita aikin office duk dacewa aikin office ga mace musulma abune wanda yake da hatsari wannan yasa maluman musulunci suka kafa wasu sharuda wadanda dole sai mace ta cikasu yake halatta agareta tayi aikin gwamnati. Ga wasu daga cikin sharudan kamar haka:_
.
_1. Mace ba zata fita neman kudi ko aikin Gwamnati ba, sai dai in Mijin nata ba zai iya ciyar da ita ba, kuma bata da wata sana'ar cikin gida wacce zatayi._
.
_2. Dole ne ya kasance aikin nata irin wanda al'ummah suke bukatuwa sosai gareshi ne Kamar misalin aikin Likita jinya, koyarwa, dinki, da sauransu._
.
_3. Dole ne ta fifita ayyukan cikin gidanta sama da aikinta na waje Wato wajibi ne ta sauke hakkin mijinta na cikin gida kafin ta fita izuwa akin._
.
_4. Dole ne ya zamanto babu chuďanya tsakanin maza da mata awajen aikin, ko kuma kebancewa da Maza._
.
_5. Idan zata fita, dole ne ta fita acikin Sutura ta Mutunci. Kuma banda biye biyen wasu guraren inda bai shafi aikinta ba._
.
_6. Dole ne ta fita akan lokaci kuma ta dawo akan lokaci._
.
_7. Dole ne ya zamanto da cikakkiyar yarjewar Maigidanta. Idan bai amince ba, dole ne ta hakura._
.
_8. kiyaye kasancewa ita kadai a cikin abin hawa daga ita sai direba ba tareda wani muharraminta a wurin ba._
.
_9. Haramunne ta sanya turare a inda wadanda ba muharramanta zasu iya jin sa._
..
_Wadannan suna daga cikin sharuddanda dole sai mace ta cikasu idan har ta cika sharudan to babu laifi tayi aikin in sha Allahu._
_A duba:_
_*Fataawa al-Mar'ah al-Muslimah (2/981)*_
..
Wallahu A'alam
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ
*ALLAH TA'ALA YASA MUDACE*
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*