Labarin Wani Dattijo



🌀Labarin Wani Dattijo👳🏾‍♂️

Babbar sallah ta gabato, kowa yana ta shirye-shiryen tanadin bikin sallah, shi ma Malam ba a bar shi a baya ba, ya tattara 'yan kuďaďensa ya nufi kasuwa don siyen ragon layya.

Da isarsa kasuwa ya zarce inda ake siyar da raguna, ya samu na dai-dai kuďinsa ya biya ya nufo gida da shi.

A hanyarsa ta zuwa gida, sai ya hadu da wani saurayi ďan unguwarsu, ya roke shi da ya amshi wannan ragon ya wuce masa da shi gida saboda zai biya wani waje. 

Cikin biyayya wannan saurayi ya amshi rago ya nufi gidan wannan dattijon malami. To dama gidaje biyune a jere kuma kusan irinsu ďaya, sau saurayin nan ya rasa gane wannene daga ciki gidan malam, kawai sai ya shige na farkon.

Da shigarsa gidan ya tarar da wata māta da yaranta guda uku, ya yi sallama suka gaisa, ya ce ga rago nan malam ya ce a kawo maki.

Ashe fa ita wannan māta makociyar malam ce, mijinta ya rasu shekaru uku baya yā bar ta da yara 'kanana guda uku.

Da jin haka mata ta kama murna tare da godiya, yara kuwa tuni sun soma tsalle-tsalle suna murna zā su ci nama da sallah. Allah Sarki!

Yayin da mai gida ya dawo gida, tun a zaure ya ji be fara jin kukan rago ba, ya shigo gida be ga rago ba, 😁 ya tambayi matarsa “Hajiya ina ragon yake ne”?

Matarsa ta canja fuska ta ce wani rago kuma? Ya ce wanda na aiko da shi mana. Ta ce to lallai dai ba a shigo nan gidan da rago ba, amma ďazu ina ji yaran can gidan suna murna an kawo masu rago, da alamu can gidan aka zarce da shi, sai ka yi marmaza ka je ka amso shi kafin su yanka shi. 

Malam ya ce a bar masu kawai. Hajiya ta ce inaa! Mu kuma fa? Malam ya ce a yadda wadancan marayu suka shiga cikin farinciki, idan na yanke masu shi tabbas ban yi wa kaina adalci ba.

Malam ya tuna da wani wanda yake bi bashi, ya nufi wajenshi ko zai samu a biya shi don ya dubo wani ragon koda 'karami ne. Aka yi sa'a kuwa wancan mutumin ya ce dāma na gama haďa maka kuďinka ina jiran mu hadu in ba ka, cikin farin ciki ya amshi kuďi ya nufi kasuwa.

Kafin isarshi wajen da ake sayar da raguna, wani ya ba shi shawarar ya nufi hanyar shigowa kasuwa ya tsaya, idan 'yan 'kauye masu kawo rago don su sayar sun zo sai ya siya, domin an fi samu da sauki a wajensu.

Haka kuwa aka yi, da zuwansa bā da jimawa ba sai ga motar raguna. Mai mota ya tsaya aka fara saukar da raguna, malam ya hangi wani rago 'kosasshe da ya burge shi, duk da ya san ba shi da kuďinsa, ya je ya dafa shi yana ci gaba da kallon shi.

Mai rago ya zo ya ce malam zā ka siya ne? Cikin murmushi malam ya ce wannan kam yā fi 'karfina. Mai rago ya ce ka je da shi na ba ka shi kyauta saboda Allah.

Mai rago ya ce, a kan hanyar zuwanmu nan, motarmu ta 'kwace mana, ta yi ta juyawa kamar zā ta kife da mu. Sakamakon addu'a, sai Allah Ya kare mu, ko rago ďaya be jikkata ba, saboda haka na yi alkawarin idan muka isa gari, duk wanda ya fara dafa ragona zan ba shi kyautarsa.

Cikin farinciki malam ya yi godiya ya jā rago ya tafi gida. Allahu Akbar!
.
.
*Darasi:*

— Ita kyautatawa ba ta da sakamako face kyautatawa.

— Duk wanda ya taimaki wani, tabbas Allah Zai taimake shi. 

— Idan ka ji tausayin na 'kasa da kai, Allah Wanda Yake a sama Zai taimake ka.

Allah Ya sa mu dace.
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*(Ansar).*

*📚Irshadul Ummah whatsApp.*
*08166650256.*

https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)