NASIHA GA DALIBAN ILIMI.



NASIHA GA DALIBAN ILIMI.

Yadda rayuwa ta kasance.

Bayan kammala kandi....
Duka abokan karatu kowa yakama gabansa ta hanyoyi daban daban a rayuwa.

Wasu sun gama jami'a har sunkai matakin:
Professors,
Doctors,
Engineers,
Teachers,
Pilots,
Lawyer,
Administration,
Imams,
Pastors,
Ministry over_seer
Business tycoon e.t.c

Wasu sunyi aure,har sun haihu, 
Wasu najiran yadda lamarin ubangiji zai kaaya.
Wasu sun mutu,karmu manta wannan.

Wasu kuma ciwo ya kwantar dasu, wasu kuma anachan ana karatun digri wasu harda digirgir.

Wasu kuma ko gurbin karatu basu samu ba (admission) a makarantun gaba da sakandiri,kuma ba halin yi.

Wasu kuwa har takaiga suna da kamfanin kansu,
Wasu kuwa sune masu ruwa da tsaki a kamfanoni na duniya.

Amma ya kakeji idan ka hadu da abokin karatunka a baya, musamman idan yacimma muradinsa kaiko ko kusa da hakan baka kaiba?
Tunanin abubuwa da dama zasuzo maka a zuciya koh ?
Amma bawai ubangiji ya manta dakai bane.

Kayi tunanin wadanda suke yawo a titi da kaya masu datti kuma yagaggu kuma suke rayuwa a haka,zakace ubangiji ya manta da kai? Na tabbata wanchan tunanin zaibar zuciyarka.
Karka manta wasu ma sun mutu.
Dabi'ace ta Dan_Adam yayi kishi ga sa'aninsa wanda suka fishi a rayuwa,amma hakan baida wata fa'ida.

Ba wani DANASANI,kowa da hanyar dazai cimma manufarsa a rayuwa kuma nisan ba daya bane.

Wasu zasu isa da wuri kafin kai wasu kuma zaka riga su,amma a kowane mataki a tsinci kanka a rayuwa,kadaure ka cigaba,akwai *Nasara*.

Kataya wanda sukai nasara murna,hakan na nufin cewa naka na tafe a hanya.

Abokinka ya saya mota,tayashi murna.
Katuna cewa zaka siya taka, la'alla lokacin da akadena yayin tasu. 

Rayuwa ba gasa bace, karka riqa tsere da wani.katuna,zamu iya karanta takadda daya amma baabi daban daban a lokaci daban daban.

Abinda da kake ciki a yau ,rubutashi,saboda duniya zata karanta gobe,zai kasance wani sashi na labarin nasararka.

Bawani wuri da bazaka iya kaiwa ba,kayarda da kanka ,kasan manufarka,kasan rauninka,kuma kaciga da dagewa.

Ka koyar da kanka,saboda abinda yakai wasu nesa,saa lokacinsu sukai suka gina.

Karka damu da nasarar wasu,sararin samaniya yana da girma sosai ga tsuntsaye batare da sunyi gogayya da juna ba.

Ka muhimmanta duk wani qanqanin abu daka samu,ka abi dokokin ubangiji.
Domin da Allah, komai zaka cimma wa.

Ga wadanda suka cimma muradinsu,karku manta da na qasa daku,saboda rayuwa juyi_juyi ce,wanda ka taimaka mawa yau, la'alla gobe shi zai riqe hannunka ya taimaka ma.

Daga:
Abubakar Mustapha Daura,
ASOF member.
©️ ASOF 2021.
Post a Comment (0)