RANAR ARFAH DA FALALARTA



RANAR ARFAH DA FALALARTA

_Assalamu Alaikum 'yan uwa musulmi,Wannan tunatarwa ne akan Wannan Rana Mai Albarka fisabilillah._

Manzon Allah ﷺ yace:
*(Babu wani yini da Allah yafi yawanta yanta bayinsa daga Wuta zuwa aljanna,kamar yinin ranar Arfa,kuma Lallai Allah yayi yin dubi zuwa ga bayinsa sai yacewa Mala'ikunsa,Minene Wadan can bayin nawa suke buqata??)*
@صحيح مسلم(1348)

Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Mafi alkhairin addu'a itace adduar ranar Arfa,Mafi alkhairin abinda na fada ni da sauran Annabawa kafina shine;*
ل*ا إلَهَ إلَّا اللَّهُ وحدَهُ لا شريكَ لَهُ، لَهُ الملكُ ولَهُ الحمدُ وَهوَ على كلِّ شَيءٍ قديرٌ)*
@حسنه الألباني في صحيح الترمذي رقم (3585)

Manzon Allah ﷺ yace;
*(Yin Azumin ranar Arfa ina sa ran Allah zai kankare zunuban shekarar da tagabata da shekarar bayanta)*
@صحيح مسلم(1162)

Nana A'isha رضي الله عنها tana cewa;
*"Babu wata rana acikin shekara da azumi acikinta yafi soyuwa a gareni kamar Azumin Ranar Arfa"*
@صحيح مسند ابن الجعد (٥١٢).

Allah kasa mudace,Allah ka gafarta mana Allah Kai Mana rahma Allah ka datardamu Allah kasa muna Cikin bayinka da zasu Dace dunya wal akhirah Amin.



*'YAR MUTAN DIKKAWA CE✍🏼*
Post a Comment (0)