RANAR TARA GA ZUL-HIJJAH. RANAR ARFA



RANAR TARA GA ZUL-HIJJAH. RANAR ARFA

Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga cikamakin Annabawa, da alayensa da sahabbansa da wad'anda suka tafi a kan tafarkinsa har ya zuwa ranar sakamako. Bayan haka:

Ya ku bayin Allah, yana da kyau ku sani ce wa. Ranar Arfa yini ne da aka san shi da falala da yawan lada, da gafarta zunubai. Shi yini ne mai girma, ana sanin ma'abotansa da tauhidi, domin suna fad'an: La'ilaha Illallahu, ga shi Manzon Allah (S A W) ya ce, (Kuma mafificin abin da na fad'a ni da Annabawa gabanina: Lailaha Illallahu). ya zo a cikin hadisi: (Mafificiyar addu'a ita ce addu'a ranar Arfa).

Ku yawaita salati da saama ga Annabi ( S A W), ku yawaita yi masa salati a kowane lokaci, domin hakkinsa a kanku yana da girma sosai, ku yawaita salati a gare shi domin ku sami lada mai girma, domin duk wanda yayi salati sau d'aya a gare shi Allah zai masa salati goma.

*RANAR GOMA GA ZUL-HIJJA. RANAR IDI*

Idi ya k'unshi tsarkake d'abi'u da kyautata halaye, ta hanyar kwad'aitarwa a kan hak'uri da juriya, da sa da zumunci a cikin wannan ranar, da afuwa, da tsarkake zukata daga k'ullata da hassada da gaba. Domi idi yini ne na farinciki da y'an uwantaka ta musulunci.

Annabi ( S A W) yayi umarni da sallar Idi ga maza da mata har da kulallun mata wad'anda ba al'adarsu ba ce su fita, da masu haila, domin su halarci addu'ar alheri da addu'ar musulmi, su k'auracewa wajen sallah, kada su zauna a cikin filin idin, domim filin idi masallaci ne.

Ku fito ya ku musulmi zuwa sallar idi, mazanku da matanku, yara da manya, don bauta ga Allah, da aiwatar da umarnin manzon Allah da neman alheri. da yawa alheri da kyaututtuka kan sauka a filin idi daga Ubangiji mai girma.

Da wannan nake fatan Allah ya karb'i addu'oinmu ya biya mana buk'atunmu, Allah ya sa muyi sallah lafiya mu gama lafiya. Bissalam.


*HASSANA D'AN LARABAWA* ✍️
Post a Comment (0)