SADAKAR DA TAFI KOWACCE FALALA DA DARAJA



SADAKAR DA TAFI KOWACCE FALALA DA DARAJA 

Sahabi Sa'ad bin Ubada Allah ya kara masa yarda alokacin da Mahaifiyarsa ta rasu sai yake cewa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama "Ya Manzon Allah mahaifiyata ta rasu, shin zan iya mata sadaka?? Sai Manzon Allah yace "Eh" sai Sa'ad ya ce; ya Manzon Allah wana sadaka ce ta fi falala?? Sai Manzon Allah ya ce "Shayar da ruwa". 

صحيح النسائي ٣٦٦٨

A cikin wannan hadisin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana nuna mana cewa mafi girma da darajar sadaka shine ka shayar da mutane ruwa, imma ta hanyar tuna rijiya ko tona bore hole, ko sayan ruwa a ajiye a masallaci ko wani wuri da mutane ke taruwa dama sauran hanyoyi na shayar da mutane ruwa.
   Haka kuma acikin wannan hadisin Manzon Allah yana kwadaitar damu akan yiwa mamatanmu sadaka domin ladan ya riskesu.

*Kada mu manta da iyayen mu cikin wannan wata mai albarka, nema musu Rahmar Allah da kuma yi musu sadaka ladan ya riske su*

Allah Ta'ala ka yi Rahma ga iyayen mu ka jikan su da sauran musulmi baki ɗaya. 

# Zaurenfisabilillah 

Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)