TAMBAYA❓
:
Shin wai dole ne idan mace za tayi wankan haila sai ta tsefe kitson da ke kanta?
:
*AMSA*👇🏻
:
Dukkan Malamai fuƙaha'un da ke Mazhabobin nan guda huɗu wato:
:
Hanābila
Mālikiyya
Shāfi'iyya
Hanafiyya
:
Gabā ɗayansu sunyi Ittifāƙi akan cewa wājibi ne akan mace ko namiji idan yazo yin wankan tsarki ya game dukkanin jikinsa da ruwa, saboda faɗin Mαnzon Aʟʟαн(ﷺ) cewa:
:
"إن تحت كل شعرة جنابة، فاغسلوا الشعر وأنقوا البشر" (رواه أبو داود)
MA'ANA:
Lallai a ƙarƙashin kowanne gāshi (na jikin mutum) akwai janaba, danhaka ku wanke kai kuma ku tsarkake (wanke) fāta.
:
Hakanan Mālamai sunyi ijmā'i cewa ba wajibi ne mace ta tsēfe kitsonta idan za tayi wankan janaba, sai dai Mālamai sunyi saɓani ne akan idan mace za tayi wankan haila, shin dole ne sai ta tsēfe kitsonta ko kuma a'a? An samu ra'ayoyin Mālamai akan haka:
:
(1)-Ƙauli na farko shi ne Mazhabin Mālikiyya da Shāfi'iyya sun tafi akan cewa ba wajibi ba ne sai mace ta tsēfe kitsonta. Hujjarsu kuma itace, sun dogara ne akan waɗansu Hadīsai da kuma āsār na Sahabbai da aka ruwaito.
:
(2)-Ƙauli na biyu shi ne, Mazhabin Hanābila da Zāhiriyya sun tafi akan cewa wajibi ne mace ta kwance kitsonta idan za tayi wankan haila. Daga cikin dalilansu sun kafa hujja da wannan Hadisi da Mαnzon Aʟʟαн(ﷺ) Yace da A'isha:
:
"إنقضي شعرك واغتسلي" (رواه إبن ماجه)
MA'ANA:
Ki kwance gāshinki sannan kiyi wanka.
:
To sai dai mafi yawan Mālamai sun ɗauki wannan Hadisi ne a matsayin cewa Mustahabbi ne mace ta tsēfe kitsonta, sukace domin wannan Hadisi na A'isha a cikinsa babu hujjar cewa wajibi ne sai mace ta tsēfe kitsonta, saboda ba wai a lokacin wankan haila ba ne Annαвι(ﷺ) Yace da ita hakan ba, ya faɗi haka ne a lokacin da take cikin harama da aikin hajji kuma tana cikin yin al'ada.
:
Shiyasa mafi yawa daga cikin Mālamai sun tafi ne akan cewa indai har Mace zata zuba ruwa a kanta kuma ya shiga cikin kanta sosai har ya taɓa fatar kanta, to ba dole ba ne sai ta kwance kitson da ke kanta ba. Amma idan ruwan ba zai samu damar shiga cikin kanta ba in ba ta kwance ba to a nan ya zama wajibi a kanta sai ta kwanceshi.
:
Danhaka dai idan an haɗa dukkan Hadīsai da kuma āsār ɗin da sukazo akan wannan Mas'ala, sai Mālamai sukace magana mafi inganci itace mustahabbi ne kwance kitso a wankan haila ba wai wajibi ba ne, domin dama babban abinda ake buƙata dai shi ne ruwa ya samu shiga cikin kai sosai yadda zai iya taɓo fatar kai shikenan wanka yayi.
:
Domin kuwa ko da mace ta tsēfe kitsonta indai ba ta zuba ruwa ya shiga cikin kanta ba sosai to wankanta bai yiba, danhaka ba wai tsēfewar ake kallo ba, shigar ruwa cikin gāshi ake kallo, idan ya zamana ruwan ba zai shiga ba har sai in an tsēfe gāshin, to anan tsēfewa ta zama wajibi kenan.
:
WALLAHU A'ALAM.
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248