SHIN WANI AIKIN ALHERI KA KE YI, KO KAYI TSAKANINKA DA ALLAH, WANDA KODA BAYAN RAYUWARKA LADAN ZAI RIƘA ZUWA GARE KA?
Hadisi ya inganta daga Sahabi Anas ɗan Malik radiyallahu anhu ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce: "Abubuwa guda bakwai ladarsu na riskar mutum a cikin ƙabarin sa bayan mutuwar sa: Wanda ya koyar da ilimin, ko ya gina dam, ko ya gina rijiya, koya dasa dabino (zamanin Annabi dabino shi ne kayan icen da ake yawan ci, a yanzu kuwa dukkan wasu itacen da ke shan ƴaƴansu sun shiga ciki), ko ya gina masallaci, ko ya gadar da Alƙur'ani, ko ya bar ɗa naƙwarai yana yi masa addu'a bayan rasuwar sa". Malam Albany ya inganta shi a cikin sahihul jami'i lambar hadisi na: 3596.
Ina roƙon Allah Subhanahu Wata'ala ya taimake mu wurin gabatar da ayyukan alkhairi kafin mutuwar mu.
*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*
