TAMBAYA AKAN AZUMIN LITININ DA ALHAMIS



*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum Dan mallan azumin Monday da Thursday da akeyi menene asalin shi kuma idan mutun yayi wani irin lada ake bashi? Misalin ladan da zai samu ?

*AMSA* 👇

 Na farko dai manzon Allah saw ya sunnatar da wannan Azumin a Rayuwar sa Har ya Koma Ga Allah. Kinga kenan Sunnah Ne yin Wadannan Azumin.
 Na biyu kuma manzon Allah saw yana yin Azumin litinin ne Sabida a Ranar ne aka Haifa shi. Sai Nace shiyasa Nake Yin Azumin Ranar Litnin. Sabida Murna da Ranar da Aka Haifeni, Murna da Ranar da Na zo Duniya. Wannan kenan ya nuna Mana cewar duk wanda zaiyi koyi da Manzon Allah saw Azumi Zaike yi a duk Ranar Litinin. Kamar yadda Haka yake yi har Ya Bar Duniya.
 Haka zalika an tambayi Manzon Allah saw Akan Azumin Ranar Alhamis da yake yi. Sai Yace Ina Yin Azumi a Ranar Alhamis Ne, Sabida a duk Ranar Alhalin Ne Ake Tattara ayyukan Bayi Na Sati guda a tafi Sama Dasu ya Zuwa ga Allahu Subhanhu Wata'ala. Shiyasa Nake yin Azumi duk Ranar Alhamis Domin a tafi da Ibada ta na wannan satin Alhalin Ina Yin Azumi.
 Sannan Kuma Manzon Allah saw Yace, Ladan Azumi Allah ne da kansa yake Rubuta shi. Sabida Tsabar yawan Ladan Wannan Azumin Allah bai wakilta wani Mala'ika ya Rubuta shi ba. Ubangiji Allahu Subhanahu Wata'ala da Kansa yake Rubuta Ladan Mai Azumi.
 Sannan Manzon Allah saw Yace Duk wanda yayi Azumi guda daya Sabida Allah. Allah zai Nisantar da Fuskarsa daga shiga Wuta Na Tsawon Tafiyar Shekara Dari Biyar.
  Sabida Haka, Duk wanda Allah ya Bashi Iko. Sai ya Kula da yin Wadannan Azumummuka Guda biyu. Sabida Neman Dacewa a Ranar Tonon Asiri.
 Domin Manzon Allah saw Yace a Cikin Aljannah Akwai Wata Koda da Ake Cewa AR-RAYYAN Babu Mai shiga ta Cikinta Sai Mai Azumi. 
 Allah Da Kansa zai Kira Masu Azumi, zai ce INA MASU AZUMI? Zasu ce Gamu ya Allah. Sai Allah Yace da su KU SHIGA TA WANNAJ KOFAR.
  Sannan Manzon Allah saw Yace AZUMI ZAIYI CETO A RANAR ALKIYAMA. ZAICE YA UBANGIJI, INA NEMAN CETON WANNAN BAWA NAKA. YA BAR CI DA SHA DUK SABIDA NI. SAI ALLAH YACE AN BAKA CETON SA.
 Allah ya sa Mu cika da Imani.
 Sabida haka Sai Mu Daura Niyya. Daman dai kowa ya san bauta ta kawo mu wannan duniya. Sabida haka wanda yake da Iko sai ya dage.

Allah Shine Masani.
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)