TSAKANIN SO DA SOYAYYA //01



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*💝💞TSAKANIN SO DA SOYAYYA //01💝💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

Ana ta qoqarin rarrabe ma'anonin kalmar (so) da ta (qauna), duk da cewa su biyu din suna yin aiki ne iri guda, kuma ta kowa ce fuska, a kowani irin yanayi, maza da mata, yaro da babba kowa yana iya juya kalmomin yadda yake so, tamkar yadda suke a tsakanin masoya guda biyu, inda a nan ne ma suka fi shahara.
.
Kalmar (so) tana matsayin {suna} ne, wato kamar ka ce "In da SO da qauna", takan tsaya kuma a matsayin (aikatau) ma, kamar ka ce " Ai kuwa ya SO ta tsakani da Allah" ita ma {qauna} takan tsaya a matsayin (suna) misali: " Wato ita QAUNA ta gaskiya ba ruwanta da bin diddigin arziqin mutum" sannan takan iya zama (aikatau) ma, misali " In kana qauna ta sabo da Allah ne, to ka zo gidammu, kuma da rana"
.
Kenan in muka lura da wadannan kalmomi guda biyu, (so da qauna) za mu gano wata hikima a cikin maganar mai-girma Ado Ahmad, Gidan Dabino, da ya sanya wa littafinsa na farko da ya yi fice, wato "In da So da Qauna", kamar dai yana nufin, inda duk so yake ne qauna ma tana nan, haka in da duk qauna take so yana nan, a taqaice dai abu guda ne, kamar ka ce "Ina son ki" ko ka ce "Ina qaunar ki" ko ka fadi ta wata hanyar "Sonta yake" wato "Qaunarta yake" ta wannan bangare ba sai mun wahalar da kammu wai ala tilas sai mun rarrabe ma'anonin kalmomin biyu ba, in muka dauki daya ma ta wadatar.
.
So, kamar yadda muka sani, wani motsi ne da yake tattare da halittu masu yaduwa ta fuskar saduwar da namiji da 'ya mace, kenan za mu iya iyakance shi da wanzuwa tsakanin Mutane, Aljanu, dabbobi, da dasauran halittu irin su: Qururai, tsutsotsi da nau'o'in tsuntsaye da ma halittun ruwa.
.
Kalmar "so" kalma ce da ta kumshi tausayi da ruhin taimako, don haka tana iya aukuwa a bangaren jinsi guda, wato maza zalla ko mata zalla, kamar yadda takan kurdada tsakanin iyaye da 'ya'yayensu ko malamai da almajiransu, ko ma 'yan uwa na nesa da na kusa.
.
In har za a kalli kalmar so da irin idanun da ya kamata, tabbas za mu fahimci cewa, ba a iya fassara ta, sai an kalli abin da ke tsakanin mai yin ta da kuma wanda ake yi masa, akan sami musayarta, wani lokaci takan zo a bangare guda, sannan akwai ta gaskiya akwai kuma ta qarya, kowacce a tsakanin wadannan tana da iyaka kuma ana iya gane ta. Ku biyo ni.

Zamuci Gaba Inshaa Allaahu Ta'aalaa

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*WhatsApp @Zauren Sunnah*
 +2348039103800.
 +2347065569254

*follow My Facebook Page*
Visit to Like my Page-https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp

*Facebook @Zauren Sunnah*
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*Telegram: @Zauren Sunnah*
https://t.me/joinchat/AAAAAFCIDJerVcs_IP1D9g

*وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت أستغفرك ونتوب إليك. وأستغفر الله لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرالرحيم*

*_والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته_*
Post a Comment (0)