WANDA YA KARƁI BASHI NA TSAWON WANI LOKACI



Tambaya
:
Mutum ne ya karbi rancen kudi tsawon wani lokaci bai biya ba har ta kai ga darajar wannan kudin ta karye, to idan zai biya shin asalin adadin kuɗin da ya karba zai biya, ko kuma ƙimar kuɗin zai bayar ta lokacin da ya karɓe su?
:
Amsa:
:
Alal-haƙiƙa Wannan wata Mas'alace da Malamai suka tattauna a kanta. Asali dai abinda a ka sani a shari'ance shi ne, idan Mutum ya karɓi bashin wani adadi na kuɗi, to zai dawo da kwatankwancin adadin abinda ya karɓa ne, ba tare da duban cewa shin ƙimar wannan kuɗin ta ragu ne ko ƙaruwa tayi ko kuma tana nan kamar yadda ta ke.

Hakanan idan wata kadarace Mutum ya karɓeta a matsayin bashi to itama zai dawo da ƙimar wannan kadara ne lokacin biya, ba za a yi la'akari da ƙaruwar farashinta ko karyewar ta ba, matukar dai a na nan a na amfani da wadannan kudaden a garin ko kuma a Ƙasar, amma idan ya kasance an yi canjin kudaden ne ya zamana an dena amfani da wancan asalin kudin da a ka karbi bashin da shi, to a nan sai Mutum ya bada kimar abinda ya karba.
:
 To amma idan misali ya kasance darajar wannan kuɗin ta karye sosai ta yadda idan da za a biya bashin a haka to shi mai asalin kuɗin zai ga kamar an cuce shi ne, hakan yasa sai Malamai sukayi saɓani a kan wannan mas'ala, mafi yawan Malaman da ke Mazhabobin Mālikiyya Shāfi'iyya Hanafiyya da kuma Hanābila duk sun tafi ne a kan cewa wanda ya karɓi bashi to zai biya ne dai dai kwatankwacin adadin kuɗin da ya karɓa ne kawai.

Misali idan ya karɓi (N1,000) rance, to idan ya tashi biya zai ba da iyakar wannan (N1,000) ne kawai, ko da kuwa darajar kuɗin ta karye ko kuma ta ɗaga sama, sai dai wani sashe na Malaman da ke Mazhabin Hanafiyya sukace in dai an samu hauhawar farashin wannan kuɗi ko kuma faɗuwar farashinsa to Mutum zai biya ƙimar kuɗin ne ta lokacin da ya karɓi bashin.

Amma wasu daga cikin Malaman Mālikiyya sukace idan hauhawar farashin ta yi yawa sosai ko kuma ta karye sosai to Mutum zai biya ƙima ne, amma idan hauhawar farashin ko kuma karyewarsa ba mai yawa bace sosai to zai biya adadin kuɗin da yakarɓa ne ba ƙimarsa zai biya ba, sukace kamar dukiyar da wani Ɗanfashi yayi ƙwacenta ko dukiyar da wani Ɓarawo ya sata to ko da shekara nawa tayi a wajensa adadin kuɗin zai biya ba kimarta ba ko da kuwa darajar wannan kuɗin ta karye, sai dai kuma a gefe ɗaya akwai Malaman da sukace Ɗanfashi dakuma Ɓarawo za su biya kimar kuɗin ne idan darajar kuɗin takarye.
:
An samu saɓani tsakanin Malaman da suka rayu a irin wannan zamanin da a ke amfani da takardu na kuɗaɗe, da kuma maganganun da Malamai sukayi akai kamar haka.
:
(1)-Ƙauli na farko wasu daga cikinsu sukace za a tafi ne a kan asali kamar yadda a ka sani idan Mutum ya karɓi bashi to zai biya ne dai dai kwatankwacin adadin kuɗin da yakar ɓa, sukace ko da darajar kuɗin ta karye ko kuma ta ɗaga sama.
:
(2)-Ƙauli na biyu kuma wasu daga cikinsu sukace idan bashin ya ɗauki lokaci mai tsawo ba a biya ba har ta kai ga darajar wannan kuɗin ta karye, to idan an tashi biya za a bayar da ƙimar darajar kuɗin ne a lokacin da a ka karɓesu, kamar Misali Mutum ne ya karɓi rancen (N1,000) ya sayi gida ya shiga, bai biya kuɗin da wuri ba sai bayan shekaru (10) ko (15) ko kuma (20), a lokacin darajar wannan kuɗin ƙila ba ta wuce a sayi ƙofofin gidan kaɗai dasu ba, danhaka sukace idan ya tashi biya to zai biya adadin ƙimar kuɗin da zai sayi irin wannan gidan ne da shi ko da kuwa alokacin gidan zai kai ƙimar (N10,000) ne.
:
(3)-Ƙauli na uku kuma shi ne Malaman da suka tafi a kan cewa idan ya kasance darajar kudin da a ka karba ta karye sosai ta yadda akwai cutuwa ta ɓangaren wanda ya bada bashin idan a kace za a ba shi iyakar adadin kudinsa da a ka karba ne kawa.

Danhaka sai Malamai sukace a nan sulhu ya kamata a yi musu a tskaninsu, mai biyan bashi ya ɗanyi ƙarin ƙimar kuɗi ko da bai kai ƙimar asalin kuɗin da ya karɓa ɗin ba, shi kuma mai kuɗi sai yayi haƙuri ya karɓa a haka ya zama an yi musu sulhu kenan kowa dai bai samu yadda ya ke so ba.
:
An samu Malamai da yawa waɗanda sukafi rinjayar da wannan kauli na uku, sukace idan har ya kasance karyewar darajar kuɗin ta kai yawan ɗaya bisa uku (1/3) ko kuma sama dahaka na kuɗin da a ka karba, sukace to abinda yafi dacewa ayi bisa ga adalci da kuma maslaha shi ne, ko dai a biya ƙimar kuɗin ta lokacin da a ka karbesu ko kuma a yi musu sulhu:

    ※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)