Wanda Ya Soki Sahabi Ku Tuhumci Musuluncinsa



Ramadaniyyat 1442 [17]

Wanda Ya Soki Sahabi Ku Tuhumci Musuluncinsa

1. Duk mai son ya rusa addini, to daga kan sahabbai yake farawa, saboda su ne a sama, idan aka taka daya daga cikinsu, to na kasansu zai su yi saukin takawa; watau tabi’ai da almajiransu, har abin ya iso kan limaman shiriya, watau Imam Abu Hanifa da Imam Malik da Imam Shafi’i da Imam Ahmad, da irinsu Sufyanu A-Sauri da Sufyan bn Uyaina da Abdullahi bn Mubarak da Ishak Ibn Rahuya, duk wadannan da ire-irensu, za su yi saukin takawa, saboda an riga an taka na sama da su.
2. Don haka Imamu Ahmad yake cewa: "Idan ka ga mutum yana fadar muguwar magana a kan wani sahabi, to ka tuhumci Musuluncinsa”. [Duba, Al-Mukhallasiyyat#2604 da Ibn Kasir, Al-Bidaya Wan-Nihaya, juzu'i na 11, shafi na 450].
3. Domin duk wanda zai yi haka, to ba ya so Musulunci ya samu daukaka, yana so ne ya rushe addinin daga tushensa. Saboda idan ya zamanto wadanda suka zauna da Annabi (ï·º) ba su samu kariya ba, har ya zamanto za a iya cin mutuncinsu, to babu wanda zai iya tsira da mutuncinsa bayansu.
4. Babu shakka makiya Musulunci sun fahimci cewa, sahabbai su ne ginshiki mafi karfi na kafuwar Musulunci da tsayuwarsa a bayan kasa bayan Manzo (ï·º). Sun gano da wuri cewa, babban abin da za su yi su girgide wannan dashe na alheri, shi ne rushe wannan ginshiki (watau sahabbai), idan sun yi haka, kuma suka yi nasara, to hakansu ya cimma ruwa. Domin tarbiyyar da Annabi (ï·º) ya yi shekaru yana yi, ta rushe, don haka babu kuma wanda zai samu wata tarbiyya da ta fi wadda sahabbai suka samu daga Manzo (ï·º), don haka idan har an yi nasarar rushe su, to ta kowa ma za ta rusu cikin sauki.
5. Duk wasu masu hankali da imani a zuciya ba za su taba sauraron wannan akida ba, ko su karkata ga wannan ra'ayi, domin girman hadarinsa ga Musulunci da Musulmi baki daya da yadda ya ci karo da ilimin da suke da shi dangane da nagartar sahabbai da hasken tarihinsu.


https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)