HUKUNCIN MACEN DA TAKE SO A SAKE TA



TAMBAYA
========
👇
Mal. Ina da baya, kamar yadda akasabayi. Mal. Dan Allah Maca ce ake zaman aure, bacuta ba cutarwa, amma has kullum burinta shine asaketa, basau daya tafara fadin hakanba, to mal.make shawara anan. Allah Jada ran mal.


AMSA
=====
👇
Idan har ta takura akan sai an sake ta. Sai a sake ta Amma dole zata Biya kudin Na KUL'I. Ma'ana zata Biya Ka Kudin da zaka sake yin wani Auren. Wannan Shi Ake Cewa KUL'I a Musulunci.
 Akwai Hadisi daga Abdullahi dan Abbas cewar Matar Sabit ibn Qais ta zo wajen Manzon Allah saw ta ce. Ya manzon Allah, Bana dorawa sabit Lefin Matsala Akan kula Addininsa ba, haka akan Iya Mu'amular sa ba. Sai dai ina Tsoron bijire Masa. (Ma'ana ba zata Iya Yimasa Biyayya ba. Sabida ba ta son Shi ) Sai manzon Allah saw Yace da ita ZAKI BIYA SHI GONAR SA DA YA BAKI A MATSAYIN GADO? Sai ta ce Eh, ZAN MAIDA MASA. SAI MANZON ALLAH SAW YA BA SHI UMARNI AKAN YA SAKE TA.  
   Sabida haka kenan, idan irin wannan ta faru. Wajibi ne zai lisaafa Abinda ya kashe ta Biya shi. Tinda itace ta nemi a sake ta. Sabida Sau da yawa, matan da aka Yiwa Saki Ukku, suna Samu Su Auri Wani daban, daga baya Sai su Tayar Musu Da Fitina Akan sai Sun Sake su. Sabida su smi Dama su Koma Gidan Mazajensu su na Baya.
 Sabida haka Idan Haka ta Faru, zata Biya ka duk Abinda ka kashe sai ka sake ta. Sai Ta yi tafiyar ta.
  Wata Matar Kuma ta Rabu da Mijinta Akan wani Abu da bai Kai ya Kawo ba. sai daga baya idan ta yi wani Sabon Auren. Sai kuma ta ji cewar wannan sabon Mijin Baya Iya gamsar da ita a shimfida kamar Wancan Na baya din. Anan kuma zai Hadu da Sharrin Mace. Sabida ya Dinga ganin Fitina Kala-kala akan sai ya saketa. Don ta samu ta Koma Gidan Mijinta na Baya. Wasu ma Har waya zata dinga Yiwa Mijinta na Baya Akan Ita fa ba ta sami wurin zama ba.
 Wanda kuma ba Mamaki shi din ma ba dadi bane yasa ya Rabu da ita ba. Sabida Hankalin ta ya dawo gare shi.
 Ko kuma Bayan ta Aureka sai take tunanin Yaramta da ta Bari a gidan Mijinta na Baya. A haka sai Tace sai ka sake ta. Ka ga Nan ma zata biya ka duk Abinda ka kashe mata. Ko tayi maka wani Auren. Domin zama da ita ba zai yiwu ba.
 Allah ya Gyara Halayen Mu...

Allah shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797
Post a Comment (0)