BAMBANCI {9}



BAMBANCI {9}

Yin riga-kafi da abubuwan da Shari'a tayi mana tanadainsa kuma ta yarda da su (kamar Azkaar din da ya gabata) shi ne garkuwa kuma maganin duk wani sihiri, hassada, maita ko kambun baka mafi muhimmanci kuma na farko da mutum zai yi domin samun kariyar Allah Ubangijin halittu gaba daya.

Amma sau da dama sai ka same mu da sakacin kiyaye su, musamman ma ga mata da kuma ƙananan yara, sai kaga yarinya karama ana barinta ba tufafi ajikinta kanta a bude ba dankwali ko hijabi, wajan kwanciya ba a yi musu addu'a a tofa kuma a shafa musu a jiki kamar yadda Shari'a ta tabbatar.

A irin haka ne sai kaga shaidanu irin su *Jinnul Aashiq (Aljanin soyayya)* ya shiga jikin yarinya tun tana karama, har ya saba da jikinta idan ta girma ma ya zamar mata alaqaqai, ya hana ta alaqa da mutane da sauran abubuwa marasa dadin ji da gani, duk kaga yarinya ta fita hayyacinta har ta rasa me ke yi mata dadi a rayuwarta. Daga cikin alamomin da ake iya fahimtar karamar yarinya na tare da Jinnul Aashiq ga kadan daga cikinsu kamar haka:

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za mu zayyano alamomin da muka sani cikin iko da yardar Allah.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu 🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)