WAYEWA KO JAHILIYYA?



WAYEWA😎 KO JAHILIYA🤥

Abubuwan da ake yi yanzu na jahiliya wanda wasu suke ganin shine burgewa da cinyewa tun zuwan musulunci aka watsar da wadannan qauyencin, Amma yanda zaka qara tabbatar da Hadisi gaskiya ne wallahi Manzon Allah (SAW) bai ta6a fadan abu kuma ba a ga abin ya faru ba.

 Hadisin Abdullahi bn Umar (RA) wanda Imam Muslim ya fitar da hadisin; Manzon Allah (SAW) yace: Addinin Musulunci ya fara ne yana baqo, kuma da sannu zai koma yana matsayin baqo kamar dai yanda ya fara. Wannan shine rayuwar da muke ciki yau, kai mai ce abi Allah wllh kallon sabon mutum ake maka wanda bai waye ba.

Kaga mace da mijinta da yaranta suna tiqan rawa suna shooting suna nuna wa duniya abin tausayi abin baqin ciki☹️. Abin da ma ba ayi a jahiliya ba yanzu yinsa ake. lokacin da Manzon Allah (SAW) yake cewa Mata kumin mubaya'a ba za kuyi zina va, Hindu bintu Uthba ta miqe tace dama *"ya tana zina ne?* Domin su baiwa ne kawai suka sani tana zina. Amma yau gashi fitar da tsiraici ya zama ado ya zama kwalliya.

Wallahi yanzu yadda ake aure a church haka musulman mu suka koma yi kuma wai ace kar ayi magana menene amfanin sanin naka kana gani ana 6arna kana shuru? *_Allahu (SWT) yace, duk al'ummomin da akayi daga farkon duniya zuwa yau Allah yace kune mafi alkhairi ku al'ummar Annabi Muhammad (SAW). Kamar wani ne ya tambayi dalili sai Allah ya fara da ( Kuna umarni da kyawawan ayyuka a tsakanin ku kuma idan kuka ga ana 6arna kuna hanawa kuna umurtan masu yi da sudai na)_* amma yau sai gashi ana shuru wasu saboda son zuciya.

*Allah ka tsare mu da iyalan mu da fadawa halaka🤲🏻*
Post a Comment (0)