YAWAITA ISTIGHFARI AWAJAN ZAMA DA YIN ADDU'A LOKACIN TASHI DAGA WAJAN ZAMA



YAWAITA ISTIGHFARI AWAJAN ZAMA DA YIN ADDU'A LOKACIN TASHI DAGA WAJAN ZAMA

Iman Hasan Ibn Hasan albasari Allah yayi masa rahama yana cewa:
*"Ku yawaita Istighfari a wajan zamanku da hanyoyinku da gidajenku da wajan sana'arku, domin ba kusan inda rahamar Allah zata sauka agareku ba""*.

Yana cikin sunnonin Annabi s.a.w yawaita istighfari awajan zama kamar yadda Abdillahi dan Umar R.A yake cewa:
*"Mun kasance muna qidawa Annabi s.a.w awajan zaman guda yana yin istighfari sau dari yana cewa:
(رب اغفر لي وتب عليَّ إنك أنت التواب الرحيم
*RABBIGHFIRLI WA TUB ALAIYA INKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM)*.
@أخرجه أبو داود (1516) وابن ماجه (3814) والترمذي (3434)

#Awata riwayar acikin Musnad Imam Ahmad daga Abdillahi dan Umar R.A yana cewa:
"Mun kasance muna qidawa Annabi s.a.w awajan zama guda yana fadar:
(رب اغفر لي وتب عليَّ إنك أنت التواب الرحيم
#RABBIGHFIRLI WA TUB ALAIYA INKA ANTAT TAUWABUR RAHEEM) sau dari a wajan zama guda"
@مسند أحمد 6/328

Àmma adduar tashi daga wajan zama shine mutum yace:
"سبحانك اللهم وبحمدك ، أشهد أن لا إله إلا أنت ، أستغفرك وأتوب إليك".

"SUBHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIKA, ASHHADU AL LAILAHA ILLA ANTA ASTIGHFIRUKA WA ATUBU ILAIKA".
 

Daga Nana Aisha R.A tana cewa:
*"Annabi s.a.w bai taba zama awajan zama ba ko yayi karatun alqurani ko yayi Sallah face sai ya rufe da wannan adduar"*.
"سبحانك اللهم وبحمدك ، أشهد أن لا إله إلا أنت ، أستغفرك وأتوب إليك".

*"SUBHANAKALLAHUMMA WABIHAMDIKA,ASHHADU AL LAILAHA ILLA ANTA ASTIGHFIRUKA WA ATUBU ILAIKA"*.
@الترمذي 3/153

#Allah bamu ikon koyi da Annabi s.a.w addukkan ibadun mu.

Abu Aisha
Post a Comment (0)