MAGANIN KURAJEN FUSKA (PIMPLES).
TAMBAYA
*******************
Assalamu alaikum,Allah yagafarta malam yabada ladar ijitihadi.matar da zan aura ne pilmpus yamatsa mata afuska duk yabata fuskar shine nake son magani.kuma dan akara tayamu aduah idan alkhairi ne Allah yatabatar yasa ayi lafiya.sanan inaso ayimin cikaken bayan istikhara da alamun gane amsuwarta.Allah yakara lafiya da basira.dga dalibinka.ngd
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Ku nemo lemon tsami, Kurkur da kuma zuma mai kyau.
Ta wanke fuskarta sosai da ruwan dumi, ta goge da tsumma mai tsafta sannan ta tsaga lemon tsamin gida biyu, ta murje fuskarta dashi (akwai zafi ka'dan). Sai bayan kimanin minti biyar ta tashi ta wankeshi da ruwan dumi.
Sannan ta zuba garin kurkur din nan rabin cokali acikin zuma cokali biyu, ta gauraya ta shafa akan fuskar, ta barshi zuwa kamar minti 5 sannan ta wanke. Idan ya bushe ta shafa man zaitun.
In sha Allahu kurajen fuskar zasu mutu, kuma duk wani tabo ko baqi-baqi zai washe daga fuskarta.
2. Idan mutum yayi istikhara wacce Manzon Allah ï·º ya koyar, ba wani mafarki zai yi ba. A'a zai ga Ubangiji yana Qara masa so da Qauna da nutsuwar zuciya game da abinda yayi addu'ar akansa (idan akwai alkhairi gareshi cikin wannan abun).
Idan kuma babu alkhairi cikinsa, mutum zai ji zuciyarsa tana Qin abun, tana Qara rabuwa da abun ne. Kuma ana iya maimaita yin istikharar gwargwadon hali.
WALLAHU A'ALAM.