Ramadaniyyat 1442H [5]
Sahabbai: Hanya Daya Tilo Ta sanin Addinin Allah
*1.* _Wadannan mutane *(sahabbai)* su ne wadanda suka yi dakon wannnan addini na Musulunci, suka kiyaye shi, suka tsare dukkan wata koyarwa ta *Annabi (ﷺ),* tun daga kan Alku’ani wanda suka karanta daga *Manzon Allah (ﷺ),* suka kuma haddace shi. Hakanan maganganunsa da ayyukansu da sauran bayanansa, duk su ne waxanda suka nakalto wadannan zuwa ga al’umun da suka zo a bayansu._
*2.* _Da abin da suka ruwaito ne muke bautar *Allah (ﷺ).* Ta hanyarsu ne muka san Alkur'ani, ta hanyarsu ne muka san halala da haram da mai kyau da marar kyau. Ta hanyarsu ne muka fahimci akidarmu da mu’amalarmu. Duk ta hanyar sahabbai muka samu sanin wadannan._
*3.* _*Sahabban* da suke cike da amana da gaskiya, wadanda suka zama shaidun da Allah ya kafa wa al’ummun da suka gabata. Su ne *sahabban* da kowane mumini yake yi musu addu’a a kowane lokaci, kamar yadda Allah ya labarta cikin fadinsa:_
*_(Duk kuma wadanda suka zo daga bayansu suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka gafarta mana mu da ‘yan’uwanmu wadanda suka rigaye mu yin imani, kada kuma Ka sanya wata kullata a zukatanmu game da wadanda suka yi imani, ya Ubangijinmu, lalle Kai Mai tausayawa ne, Mai jin kai.”)_*
*[Hashr: 10]*
*4.* _Don haka su ne wadanda duk sanda aka ambaci wani daga cikinsu ya zama wajibi a kan musulmi ya nema masa gafara. Saboda duk nasarar nan da aka samu cikin dan kankanin lokaci, wadda ta mamaye sassa daban-daban na duniya ta samu ne da sa hannunsu, kamar yadda *Allah (SWT) ya ce:*_
*_(Idan kuma suka yi niyyar yaudarar ka, to lalle Allah Ya ishe ka. Shi ne Wanda Ya Karfafe ka da taimakonsa da kuma muminai. Ya kuma hada tsakanin zukatansu. Idan da za ka kashe duk abin da yake bayan qasa gaba daya ba za ka iya hada tsakanin zukatansu ba, amma kuma Allah Ya hade tsakaninsu. Lalle Shi Mabuwayi ne Mai hikima.)_*
*[Al’anfal: 62-63]*
*5.* _Haka kuwa ya samu ne a sanadiyyar tarbiyar da suka samu daga *Manzon Allah (ﷺ),* wadda ta sa suka iya tunkarar dukkan wata jahiliyya a fadin duniya har suka yi nasarar kai azzaluman duniya kasa._
*6.* _Babban abin da zai qara suranta mana su wane ne sahabbai shi ne, maganar da *Rib’i (R.A)* ya yi a yaqin Kadisiyya, lokacin da ya hadu da Rustum *(Babban kwamandan sojojin Farisawa).* A lokacin daular Farisa tana cikin manyan daulolin da suke da ci gaba. Ita da daular Rumawa su ne suke kewaye da Larabawa. Farisawa suna mallakar yankin Iraki. Su kuma Rumawa suna mallakar yankin Sham. Don haka a lokacin kasashe ne da sun kai matuka wurin raya duniya da kuma rusa ta ta hanyar amfani da karfin soja. Amma sai ga mutanen da suke rayuwa a cikin sahara a tsibirin larabawa, sun shiga har fadar Rustum, a lokacin yana zaune a fadarsa da ya sa aka qawata da shimfidu na alfarma, wadanda za su sanya mutumin sahara ya ruxe ya kidime idan ya gan su. Amma a haka Rib’i ya taho a kan dokinsa yana caka mashinsa a kan shimfidar alfarma da aka yi a wannan fadar. Ya zo har gaban *Rustum,* da *Rustum* ya tambaye shi me ya fito da da ku? Sai *Rib'i* ya ce: “Allah ne ya taso da mu domin mu fitar da wanda ya ga dama daga cikin bayinsa daga bautar bayinsa zuwa bautar Ubangijin bayi, mu fitar da wanda ya ga dama daga cikin bayinsa daga zaluncin addinai zuwa adalcin Musulunci, mu fitar da wanda ya ga dama daga kuncin duniya zuwa yalwarta”._
*7.* _Haka ya rika magana da izza, dukkan abubuwan da aka zube a gabansa na kayan alatu ba su ja hankalinsa ba, ba su dame shi ba, bai san ma an yi su ba. Saboda *Annabi (ﷺ)* ya ba su tarbiya, ta yadda kowane irin abu ba shi ne a gabansu ba, yardar Allah ce kawai a gabansu._
_Rubutawa:- *Dr Muhd Sani Umar R/lemu*_
_Gabatarwa:- *Abu-Muhd*_
*_Darussunnah foundations_*
07030233318