BAMBANCI {23}


BAMBANCI {23}

QUSTUL HINDI ko UDUL HINDI 

Yana daga cikin abubuwan da suke matuƙar takurawa jinnun da ke a jikin mutum, ana amfani da shi a fannoni da dama wajan magance matsalolin jinnu da sihiri ga kadan daga cikinsu kamar haka:

1- Mai ciwon kai ko da kuwa na jinnu ne ya rika shaqa garin qustul hindi kadan.

2- Ana hada garin qustul hindi da wasu garurruka kamar su : Habbatus saudah da Albabunaj da hulbah sai kuma Haltiti wajan magance sammu ko sihirin da ke cikin mutum ko wanda yake a mara mai jawo ciwon mara na wuce misali. Yadda ake amfani da shi shi ne:

A hada garurrukan wuri guda amma Haltitin yakasance kadan kumq ba shi da yawa sai a riƙa dibar cokali 1 kullum ana zubawa a ruwan zafi kimanin kofi 1 ana sha da zuma safe da daddare. Insha ALLAHu za ayi sauyi.

2- Mai fama da ciwon Daji ko iska, sai ya sanya qustul hindi a ruwan zafi rabin kofi sai ya zazzage rabin kwalbar Konfo a ciki sai sha ruwan, duddugar kuma sai ya goga a inda ya kumbura ko yake yi masa ciwon.

HABBATUS SAUDAH

Nassi ya yi bayanin amfaninta wajan magance cututtuka banda mutuwa da kuma tsufa, itama tana da gari, ya'ya da kuma Mai, duk ana Amfani da kowanne daga ciki wajan magance matsalar shafar jinnu ko wanne irin nau'in jinnu ne da kuma sihiri har ma da wasu cututtukan zamani cikin iko da yardar Allah Kuma a samu waraka. insha ALLAHu za muyi bayanin yadda ake hada su a rubutu nagaba.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)