BAMBANCI {29}



BAMBANCI {29}

Lallaikam duk wanda ya kauracewa ambaton Allah a matsayin wanda zai iya bashi kariya kuma wanda zai iya amintar da shi daga dukkanin abin cuta da cutarwa anan duniya da gobe alkiyama, sai kaga Allah ya sanya masa Shaiɗan a matsayin aboki ko amini wanda ko da yaushe suna tare.

Za ayi miki kishiya kinqi mikawa ALLAH kukan ki cewa: Idan har karin auren nan da mijinki zaiyi akwai Alkhairi a gareki da zamantakewarku, to Allah ya tabbatar da auren, idan kuwa babu Alkhairi to ALLAH ya wargaza lamarin. Amma duk sai ki shiga damuwa har wasu shedanun kawaye su rika zuga ki, ki kama biye-biye da shige-shigen bokaye da zai kai ki ya baro kuma ya tsunduma ki cikin damuwar da za ta hanaki zaman lafiya a rayuwarki.

Yanzu a irin haka mai zai hana aljanun su zama abokananki, ko da yaushe kima tare da su saboda ba kya tare da Allah, kiyita fuskantar cututtuka kala-kala marasa jin magani? Ina kuma ga ita wacce za ayiwa asirin tana Azkaar ko da yaushe tana neman tsarin ALLAH daga sharrin irin ki, ai kam akarshe dai dara ce za taci gida, domin dawowa kanki zaiyi, Allah ya kyauta.

Shi yasa wasu cututtukan da za kaji ance asibiti ba bu magani ko anyi awo amma anga ba abinda ke damunki/ka, to da alama akwai sihiri ciki ko hassada ko kuma kambun baka da sauransu, ta hanyar kaikayi me komawa kan mashekiya ko kuma sakacin yin Azkaar da rashin neman kariyar Allah wajan dukufa da yin Addu'a, sadaqa da kiyaye dokokin Allah. Amma dukkanninsu sai da izinin ALLAH suke tasiri.

Kowa ya dage da Azkaar safe da yamma da kiyaye dokokin Allah daidai gwargwado, kuma ya katange kansa da zuciyarsa daga neman kariyar wani abin halitta ba kariyar Allah ba, sai kaga mutum ya zauna lafiya, kuma ya samu tsaro da kariya Saboda cikakken mai bayar da tsaro shi ne Allah ya tsare shi. Kuma an ce: *"BIN ALLAH, SHI NE MAGANIN WAYYO ALLAH."*

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)