BAMBANCI {30}

 


BAMBANCI {30}

Makobcinka ne a kasuwa amma sai kaga ka kai sunan shi gidan wani boka da sunan kana so a rikita masa lissafi, ko a qaqaba masa hasara a kasuwancinsa, bai taka maka ba kuma bai zubar maka ba, kawai saboda muguwar hassadar da ke cike da zuciyar ka. Kaicoo...

Ina ma ace ka roki Allah wanda yake ba shi kasuwa da sanya albarka a kasuwancinsa kai ma sai yabaka saboda shi ne mai bayarwa ga wanda yaga dama, na tabbata ya fi maka alkhairi da biye-biyen bokayen nan da kake yi, suna karbe maka kudadenka kuma ka kasa samun nutsuwa a rayuwarka a karshe kuma maganin da kake yiwa dan uwanka shi ne zai dawo kanka sai ka haukace ko Kuma jinnun su takura maka su hana ka sakat.

Ko kuma sai kaga mutum ya kai sunan matar da yake so ya aura wajan wani boka ko ita ta kai sunan sa wajan wani boka ko kaga matar aure ta kai sunan mijinta wajan boka, duk nan wai saboda a samu a mallake shi ko ya samu ya samu soyayyar ta.

A ƙarshe kuma sai kaga maganin ya lalace, komai ya rikice har ya fi baya rikicewa, ba nutsuwa, ba kwanciyar hankali, Aljanu nan da akayi aikin da su su dawo kanki ko kanka suyi ta ba ku bakar wahala, da ku da zaman lafiya kuma kunyi bye-bye kenan sai wani ikon Allah, a gobe alkiyama Kuma Allah na jiran ku saboda kunyi masa shirka.

Duk wadan nan abubuwan da ma wasun su suna daga cikin abubuwan da suka addabi al'ummar mu kuma suke sabbaba yaɗuwar jinnu atsakaninmu saboda an gayyato su kuma ana hulda da su, ga sakacin da akeyi wajan bin dokokin Allah da kuma rashin yin Addu'o'in neman tsari da Addinin mu ya koya mana a wurare mabanbanta.

Insha ALLAHu za muci gaba a rubutu nagaba .

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)