BANBANCIN MAFARKIN JINNU DA NA AL-ILHAMI



BANBANCIN MAFARKIN JINNU DA NA AL-ILHAMI
 .
*_TAMBAYA_*❓
:
_Assalamu alaikum_ _Malam wata baiwar Allah ta aikoni da tambaya tace takasance batada aure amma wani lokaci takanyi mafarki kamar taga tsiraicin wani ko tana mu'amula da wani a gabanta kuma mafarkin saitaji dadi Kuma idan tatashi takanga wani farin abu mai yauki_
_To Malam dan Allah kayi mana bayani meye hukuncin wannan ruwan Kuma meke kawo mafarkin._
:
_*AMSA:*_👇🏻
:
_Wannan Mafarki yana faruwa ne a bisa dalilai guda biyu._
_(1). Mafarki ne na shaidanin Aljani *Jinnul Aashiq* (Namijin dare)._
.
_(2). Mafarki ne da Allah ya sanya shi ajikin Dan Adam dalilin karfin sha'awa._

_*1. Jinnul Aashiq (Namijin dare)* Idan wannan mafarkin tana yawan yinsa ne a koyaushe, to akwai alamar jinnul Aashiq a tareda ita._
_Matsalar jinnul Aashiq ana maganinsa ta hanyar yin ruqyah kamar karanta suratul fatiha kafa 7 ana karatu numfashin karatun yana sauka acikin ruwa a hada da garin ganyen magarya guda 7 ta rika wanka da ruwan. Haka kuma a rika karanta suratul baqarah acikin gidan, shaidanun aljannu basa zama a gidan da ake karanta suratul baqarah. Haka kuma ta rika wanka da ruwan sama yana korar shaidanun aljannu daga jikin mutum._
.
_*(2). Mafarki na gaskiya.*_
_Wannan mafarki ne Da Allah ya sanya shi a rayuwar Namiji da Mace wadanda suka balaga. Wannan shi ake kira *Al-ihlaam* a larabce. Yinsa ba haramun bane, kasancewar yana faruwa ne acikin bacci. Wannan mafarkin yana faruwa ne dalilin karuwar sha'awa a jikin Dan Adam. Kuma idan mutum yayi wannan mafarkin har ruwa ya fito, to wankan janaba ya wajaba akansa. Da mace da Namiji duk suna yin wanka idan akayi mafarkin. Kamar yadda Hadisai suka tabbatar._

*_ﻋﻦ ﺯﻳﻨﺐ ﺍﺑﻨﺔ ﺃﻡ ﺳﻠﻤﺔ: ﻋﻦ ﺃﻡ ﺳﻠﻤﺔ ﻗﺎﻟﺖ: "ﺟﺎﺀﺕ ﺃﻡ ﺳﻠﻴﻢ ﺇﻟﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻘﺎﻟﺖ: ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻻ ﻳﺴﺘﺤﻴﻲ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻖ ﻓﻬﻞ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﻣﻦ ﻏﺴﻞ ﺇﺫﺍ ﺍﺣﺘﻠﻤﺖ؟ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ: ﻧﻌﻢ ﺇﺫﺍ ﺭﺃﺕ ﺍﻟﻤﺎﺀ، ﻓﻐﻄَّﺖ ﺃﻡ ﺳﻠﻤﺔ ﻭﺟﻬﻬﺎ ﻭﻗﺎﻟﺖ: ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻭ ﺗﺤﺘﻠﻢ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ؟ ﻗﺎﻝ ﻧﻌﻢ ﺗﺮﺑﺖ ﻳﻤﻴﻨﻚ ﻓﺒﻢ ﻳﺸﺒﻬﻬﺎ ﻭﻟﺪﻫﺎ؟"._*
*_ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏(130)_* *_ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏(313‏)._*

_An karbo Daga *Zainab bint Umm Salama* daga *Umm Salama* tace: *Ummu Sulaim* tazo wajen *Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam)* sai tace " Ya Manzon Allah, lalle Allah, baya jin kunya wajen gaskiya, shin mace zatayi wanka idan tayi mafarki (wet dream)? Manzon Allah yace: Eh idan taga ruwa (idan tayi inzali). Sai *Ummu Salama* ta rufe fuskarta, sannan tace: shin mace na yin mafarki (erotic dream)? Yace: Eh, hannunki ya bade da qura, ta yaya danta yake yin kama da ita?._
_*(Bukhari, 130), (Muslim, 313).*_
.

*_ﻭﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻗﺎﻟﺖ: ﺳﺌﻞ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻦ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻳﺠﺪ ﺍﻟﺒﻠﻞ ﻭﻻ ﻳﺬﻛﺮ ﺍﺣﺘﻼﻣﺎ ﻗﺎﻝ ﻳﻐﺘﺴﻞ ﻭﻋﻦ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻳﺮﻯ ﺃﻧﻪ ﻗﺪ ﺍﺣﺘﻠﻢ ﻭﻟﻢ ﻳﺠﺪ ﺑﻠﻼ ﻗﺎﻝ ﻻ ﻏﺴﻞ ﻋﻠﻴﻪ ﻗﺎﻟﺖ ﺃﻡ ﺳﻠﻤﺔ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻫﻞ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺗﺮﻯ ﺫﻟﻚ ﻏﺴﻞ ﻗﺎﻝ ﻧﻌﻢ ﺇﻧﻤﺎ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﺷﻘﺎﺋﻖ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ"._*
*_ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ‏(113) ﻭﺃﺑﻮ ﺩﺍﻭﺩ ‏( 236 ‏)_*
.
_Kuma an karbo Daga *Nana Aishat* tace: An tambayai *Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)* akan mutumin da yaga (sanyin) ruwa, amma baya iya tina sanda yayi mafarkin, (Manzon Allah) yace (Mutumin) "zaiyi wanka". An tambayeshi akan mutumin da yayi mafarki amma bai ga ruwa ba, *(Manzon Allah)* yace "Babu wanka gareshi". *Umm Salama* tace: Ya Manzon Allah idan mace taga haka zatayi wanka? Yace: Eh mata yan uwan mazaje ne._
_*(Tirmizi, 113), (Abu Dawuda, 236).*_
.
_Alal-Ajlaani yace: Ibn Qattaan yace:_ _Isnaadinsa daga Aishah da’eefi ne, amma isnaadinsa daga Anas sahihi ne._
_*Kashf al-Khafa, 1/248)*_
.
_Saboda haka idan mace tayi mafarki kuma taga ruwa, to hukuncinta shine tayi wankan janaba._
:
```Allah ta'ala yasa mudace```
:
_*©​​✍🏽 ​​Sadeeq Ñagogo{βluñgu}​​​​*_
:
_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)