CIWO YAYIN YIN HAILA
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Qai.
Na nufi yin wannan rubutun ne, don karar da yan uwa mata ilimi da mu kanmu dukka akan abinds ya shafi rayuwar mace.
Duk da cewa sanannen abu ne jin ciwo a lokacin da mace ke haila ko gama hailanta, wanda ya danganta ga yanayin ita macen, yasa na zurfafa bincike sahihi, da kuma tambayar masana a fannin don kaucewa kuskure, Alhamdulilah, na tuntubi wata babbar likita mai suna _Debra Rose Wilson_ ta hanyar _healthline_ wani website da nake bibiyarsu tun 2019, wanda suna bada updates akan cututtuka da maganinsu, kuma idan kayi sa'a sukan hadaka da likita online kai tsaye kuyi magana, duk da akwai charges a yin hakan. To saboda amana ta ilimi yana da kyau ka bada taqaitaccen tarihin wanda ka sami ilimi a wajensa, saboda haka ita malama Debra ma'aikaciyar lafityace babba da tayi karatu a fannin lafiya iri iri, kuma tafi shekara 20 tana duba da bibiyar harkan lafiya ta online wajen taimakawa mutane. Saboda tsawon rubutu, zaa iya duba website din _healthline_ don ganin cikakken bayani akanta.
To ALLAH dama ya fada mana cewa, *"Ku tambayi Masana idan kun kasance baku sani ba"* wannan aya kadai ta isa madogara da hujja a garemu, don mu fadada ilimin mu da karatunmu akan abubuwan da bamu da ilimi akan su.
Kuma wani dogaro da ya kuma bani karfin gwiwa wajen yin wannan rubutu shine cewa' *"ALLAH baya jin kunyar bayyanar da gaskiya"* da kuma inda _Nana A'isha take cewa: "Allah ya jikan MATAN MADINA kokadan *KUNYA* bai taba hanasu neman sanin addininsu ba" Idan mukace zamuci gaba dajin nauyin tambaya ko bada amsawa saboda *KUNYA* to zamu rayu cikin jahilci, wanda wannan ba uzuri bane a wurin Allah._ ALLAH yasa mu dace.
Kai tsaye a rubutunmu na gaba zamu dora daga kan ainihin hailan, da ainihin Ciwon da yake kawota. Kuma ALLAH ne mafi sani.
_Idan an ga gyara, kuskure, karancin fahimta, musamman ga wainda suke fanninsu ne na likitanci, kofa a bude take ina maraba matuqa._
*✍️Abdullah Auwal Abdullah Abou Khadeejatu Assalafeey*
13/01/1443.
22/08/2021.
https://sirassalafeey.wordpress.com/ciwo-yayin-yin-haila/