FALALAR RANAR JUMA'AH



FALALAR RANAR JUMA'AH. 

 Ranar juma'ah yini ne mai falala a wurin Allah mai girma da buwaya,shine yinin da Allah madaukakin sarki ya zabarwa musulmi a matsayin idin sati,Wanda suka haduwa cikin shi don yin sallah da kuma sanya soyayyah a tsakanin musulmi. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace"خير يوم طلعت فيه الشمس يوم الجمعة،فيه خلق آدم عليه السلام،وفيه أخرج منها،ولا تقوم الساعة إلا في يوم الجمعة" رواه مسلم. "Fiyayyaen yinin da rana ta bullo a cikin shi,shine yinin juma'ah,cikin shi anka halicci annabi adam tsira da amincin Allah,cikin shi anka shigar da shi aljannah,cikin wannan yinin ne anka fitar da shi daga cikin aljannah,yinin kiyama bai tsayuwa sai a ranar juma'ah". Abubuwan da aka so aikata ranar juma'ah. 1. Zikiri da addu'o'i. Daga jabir Allah ya yadda shi yace,Manzon Allah yace "يوم الجمعة ا ثنتا عشرة ساعة منها ساعة لا يوجد عبد مسلم يسأل الله إلا آتاه إياه،والتمسوها آخر ساعة بعد العصر" رواه أبوا داود. "Ranar juma'ah sa'ah goma sha biyu ce, daga cikin ta akwai wata sa'ah wadda ba wani mutum musulmi da zai same ta yana rokon Allah face Allah ya bashi abunda ya Roka,Ku bide ta karshen sa'ar bayan la'asar". Nisa'i da Abu dawud suka ruwaito shi. 2. Ana son yawaita yiwa Annabi s.a.w salati a cikin Daren juma'ah da yinin juma'ah. عن أوس بن أوس رضي الله عنه قال:قال رسول الله صلى الله عليه و سلم:" من أفضل أيامكم يوم الجمعة،فيه خلق الله آدم،وفيه قبض،وفيه النفخة،وفيه الصعقة،فأكثروا علي من الصلاة فيه،فإن صلااتكم معروضة علي!!" قالوا:يارسول الله،وكيف تعرض عليك صلاتنا وقد عرمت؟، فقال :"إن الله عز وجل قد حرم على النار أن تأكل أجساد الأنبياء". رواه أحمد ومسلم manzon Allah yana cewa"daga cikin mafi falalar kwanakin Ku shine ranar juma'ah, a cikin sa ne Allah ya halicci annabi Adam,kuma a cikin shi ne Allah ya karbe shi,a cikin shi ne za'ayi busa ta daya data biyu,don haka Ku yawaita salati a gare ni,domin salatin Ku ana bijiro man da shi"sai sahabbai sunka ce,ta yaya za'a bijiro maka da shi,alhali ka zamo rududdugagge? Sai manzon Allah yace"lallai Allah mai girma da daukaka ya hana kasa taci jikin annabawa" Ahmad da Muslim suka ruwaito shi. Al imamu ibnl kayyim yana cewa"anso yawaita salaita ga annabi s.a.w ranar juma'ah, da kuma Daren juma'ah, saboda fadar mai tsira da amincin Allah "Ku yawaita salati gare in ranar juma'ah da Daren sa" manzon Allah yafi kowa darajjah,haka ranar juma'ah tafi yinin da ba ita ba,don haka salati ga annabi s.a.w a wannan rana wata Karin darajjah ce fiye da wanin wannan yinin....... 3. Anso karanta suratul kahfi. An ruwaito daga imamu nisa'i,daga abi sa'idul khudury,lallai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace"من قرأ سورة الكهف في يوم الجمعة،أضاء له من النور ما بين الجمعتين. Manzon Allah yace"Wanda ya karnta suratul kahfi ranar juma'ah, Allah zai haskaka mashi da wani haske abunda ke tsakanin juma'ah guda biyu". 4. Ana son yin wanka,sanya turare,yin kawa da mafi kyawon tufafi ga Wanda zaije masallachi. An karbo daga abi sa'idul khudury,manzon Allah yana cewa"على كل مسلم الغسل يوم الجمعة،و يلبس من صالح ثيابه،وإن كان له طيب مس منه" manzon Allah yana cewa"wanka ranar juma'ah yana kan musulmi,sannan ya sanya mafi kyawon tufafin sa,inma yana da turare to yasa". 5. Anso yin sammako zuwa masallacin juma'ah. An karbo daga Abu huraira Allah ya yadda da shi yace,lallai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace"من اغتسل يوم الجمعة غسل الجنابة،ثم راح،فكأنما قرب بدنة،ومن راح في الساعة الثانية،فكأنما قرب بقرة،ومن راح في الساعة الثالثة،فكأنما قرب كبشا أقرن، ومن راح في الساعة الرابعة،فكأنما قرب دجاجة،ومن راح في الساعة السادسة،فكأنما قرب بيضة.فإذاخرج الأمام حضرت الملائكة يستمعون الذكر"} رواه البهاري و مسلم. Manzon Allah yace "Wanda yayyi wanka a ranar juma'ah irin wankan janabah,sannan yayyi sammako zuwa masallaci, kamar yayi ibadah ne da yanka taguwa(rakumi),wanda yayyi sammako a sa'ah ta biyu,kamar yayi ibadah ne da yanka shanuwa,wanda yayi sammako a sa'ah ta ukku,kamar yayi ibadah ne da yanka rago mai kaho,wanda yayi sammako a sa'ah ta hudu,kamar yayi ibadah ne da yanka kaza,Wanda yayyi sammako a sa'ah ta biyar,kamar yayi Ibadah ne da bada sadakar kwai,idan liman ya fito kuwa,mala'iku zasu halarto,suna sauraren zikirin Allah" bukhari da Muslim suka ruwaito shi. Allah ya datar damu,daga Dan uwan Ku a muslunci"MUSLIHU DALHATU RIJAL"
Post a Comment (0)