DAMUWAR MATA



Shine damuwarku mata!!! 

Miji dai miji dai🤦🏽‍♀ ya kamata ku rabu da maza da neman hanyoyin neman daukaka wurinsu tunda mun gane bazamu samu ba, ku koma ku nutsu ku nemi aljanna ta sahihiyar hanya ku gyara tarbiyyan yaranku.

 Wallahi inda zasu mallaku da iyayenku sun mallakesu a shekarun aurensu, amma har yanzu suna kuka da halin maza

 An dinga abu daya kenan? Ku nemi yardan Allah ku zauna lafiya👏🏽

 ku rungumi yaranku sune matakin karshe da zaku shiga hannunsu, kuma duka matakan biyu ku shiga saura na karshen

 kunyi rayuwar gaban iyaye kun dandana kunji irinsa, kuna tsakiya da jin dadinsu suka nuna sun gaji daku sai kuka koma hannun mutum na biyu😭 kunje hannun na biyu kunji dadi kunsha wuya, hakanan kuketa lallabawa cikin dadi da wuya kuna hakuri da juriya da kokarin cinye jarabawarku, hannun mutum na uku shine hannun da kuke da ikon tarbiyyantar dashi gyaruwansa da lalacewarsa yanada alaqa da kokarinku, kuma wai don shiririta kun tsaya kuna ta fafutukan neman aminci a hannun da kuka kusa rabuwa dashi😭😭💔

 Rayuwar yaranku yanada muhimmanci a cikin karshen rayuwarku

 ku hadu ku ceto rayuwar yaranku, itace rayuwarku ta karshe, kuma abin tausayi itace rayuwar da zata riskeku lokacin kun gajiya babu sauran karfi a tare da ku

 Ina ganin ya kamata ku samar da hanyoyi masu tsafta ta addinin islama na rayuwar aure da mazajenku bisa koyarwa da tsarin addini, ta hanyar taimaka masu da tausayawa da zama na Amana👏🏽

Ku dawo daga rakiyar masu cewa ki zama karuwar mijinki😆 wannan maganar kaman fadinta kadai ya isa ya lalata rayuwar sunna mai inganci, bata dace da matar sunna ba,meyasa baku cewa ki zame masa matar kwarai kaman nana Aisha da nana khadijan gidan manzon Allah?

 ku rinqa suffanta tsaftataccen lamari da abubuwa masu tsafta don Allah👏🏽ku suffanta abu maikyau da abu maikyau

Abubuwa da yawa da maganganu marasa kyau suna lalata zaman aurenku baku sani ba

Sannan ku fara kokari don koyar da kunya ga yaranku mata, ku nuna masu muhimmancin kunya da tasirinta a zaman aure, don da yawanku anan nasan kunyi aure lokacin ba android phone,kunyi aure lokacin da budurwa bata iya hada ido da saurayi,kuma still nagartan aurenku a hakan bai kai na iyayenku ba....amma auren yanzu sai godiya👏🏽😆

Allah Kahadamu Dana kwarai..🤲
Post a Comment (0)