HUKUNCIN ZAKKAR KUDI



HUKUNCIN ZAKKAR KUDI

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum malam kamar gold da mata ke sayi dan kwaliya idan ya kai nawani akemasa zaka

*AMSA*👇

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Allah Mai girma da buwaya ya ce, *“Wadanda suke taskance zinare da azurfa basa ciyar dasu saboda Allah, ka yi musu bushara da azaba mai tsanani”* (Attauba : 34)
da fadin Annabi ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) *“Babu wani ma’abocin zinare ko azurfa wanda ba ya bayar da haqqisu face sai ya kasance ranar alqiyama an mayar da su alluna na wuta, a gasa su a wutar Jahannama, sannan akan goshinsa da bayansa da gefensa da su, duk lokacin da suka yi sanyi sai a sake gasa masa su, a cikin wani yini tsawonsa shekara dubu hamsin, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai ya ga hanyarsa, ko dai zuwa Aljannah, ko kuma zuwa Wuta”* [Muslim ne ya rawaito shi]

*Sharuddan Wajabcin Zakkar Kudi*

1 – Shekara ta kewayo a kansu.
2 – Cikakkiyar mallaka
3 – Su kai nisabi

*Nisabin Zakkar Kudi*

1 – Nisabin zinare shi ne Dinari ashirin (85g).
Dirhami daya na zinari = Giram hudu da kwata. Don haka lissafin nibin zinari da giram zai zama kamar haka: 4.25 × 20 = 85g na tacaccen zinari.
2 – Nisabin Azurfa shi ne Dirhami dari biyu (595g)
Dirhami daya na azurfa = 2.975g. Don haka lissafin azurfa da giram zai zama kamar haka: 2.975g × 200 = 595g na tatacciyar a azurfa.
3 – Ana qaddara nisabin kudin takarda ne a kan qimar zinare ko azurfa a lokacin da za a fitar da zakkar, idan kudin ya kai nisabin daya daga cikinsu (wato zinare da azurfa) to zakka ta wajaba.
Misali : Idan da za ce giram din zinare shi ne yake daidai da Dala talatin ta amurka to zakka ta wajaba a kan wanda yake da Dala 85×30 = 2550 na dalar Amirika.

DAGA *SHEIK ALBANY.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)